Allah ya yi wa ‘Maman Taraba’, Sanata Aisha Al-Hassan rasuwa

Daga WAKILINMU

Tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Sanata Aisha Jummai Al-Hassan, wacce aka fi sani da suna Mama Taraba, ta rasu a wata asibitin ƙasar Masar, 7 ga Mayu, 2021.

Wata majiya daga ahalin marigayiyar ce ta tabbatar wa Dateline Nigeria batun rasuwar.

A halin rayuwarta, Jummai ta yi takarar kujerar gwamanan jihar Taraba a ƙarƙashin jam’iyyar APC a 2015. Ta riƙe muƙamin minista a gwamnatin Buhari.

An haifi marigayiyar ce a Jalingo, a ranar 16 ga Satumban 1959.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *