Za a iya sace kowa a Arewa?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ba mamaki a iya sace kowa musamman in dai mutum na yawo a sassan arewacin Nijeriya da dare ne ko ma da rana tsaka. Wannan lamari na satar mutane don neman kuɗin fansa ta zama babbar masana’antar samun kuɗaɗe ga miyagun irin daji dama watakila wasu a cikin gari. Wata dabara ma da matafiya tsakanin Abuja da Kaduna ke yi ita ce bin jirgin ƙasa don kauce wa gamuwa da ɓarayin a titi a yankin nan na Rijana. Wannan dabarar ma akwai lokacin da ba ta ɓullewa don akwai labarin an sace mutane bayan sun sauka a tashar jirgin ƙasa ra Rigasa a Kaduna. Don haka wannan matsala fa ta zama ƙadandagaren bakin tulu a jefe ka a fasa tulu a bar ka ka vata ruwa.

Wani abun takaicin shi ne, duk wata dama na magana da manema labarai kan yi da masu satar mutane kan nuna su ma ɓarayin wai wani abu a ka sace mu su ko an taɓa cin zarafin su ne, shi ne suka samu sabuwar sana’a da jarin ta shi ne shan miyagun ƙwayoyi, ƙatuwar bindiga, kasada da kuma shegantaka.

Ɗaya daga fitattun ɓarayin da shi ma a ka ce abokan sa sun hallaka a kan hanyar Kaduna, Nasiru Kachalla ya ce shanun sa dubu biyu a ka cinye don haka ya rasa abun da zai kama sai wannan harka ta bayyana don haka ya auka. Kazalika daidai lokacin da ya ke buƙatar a saki mahaifiyar sa jami’an tsaro suka kama don ya nemi afuwa daga wajen ta na jefa ta halin takaici, sai a ka kashe shi. In haka ne me babbar ribar masu satar mutane ne? A nawa tunanin samun canji ne a aljihu a yi shagali na wani lokaci da fitsara sannan wani dalili ya sa a tsinci kai a kabari. Haka ne mana, don fa waɗannan varayin ba sa shakkar buɗe wuta a junan su bisa wani ɗan dalilin da bai taka kara ya karya ba.

Yanzu wani ɗan musu kawai in ya shiga tsakani sai wani ya ɗauka an raina shi a cikin su daga nan sai ya buɗe wuta ya kashe wanda ya ke ganin ya raina shi, shikenan sauran ɓarayi sai su yi dariya su riƙa yi ma sa kirari da sunan mugu ba ka saurarawa miyagu. Hatta kuɗin da kan shiga aljihun ɓarayin ba su taka kara sun karya ba don rahotanni na nuna kuɗin kan bi ta wasu hannaye kafin su iso asalin hannun masu garkuwa da mutanen na daji. Ya kamata a gano masu samarwa varayin nan makamai da ma bayanan yadda sukan rutsa da waɗanda su kan sata.

A nan za mu ce sabon ra’ayi ko matsayar wasu hukumomi cewa a daina biyan kuɗin fansa don hakan kan ƙara ƙarfafa wa ɓarayin gwiwa su ci gaba da satar mutane, ba za ta dakatar da satar ba a lokaci ɗaya, domin da zarar an sace mutum ’yan’uwan sa ba za su iya samun kwanciyar hankali ba sai sun ga an sako shi ko da kuwa za su sayar da duk kadarorin su ne don biyan fansar.

Ra’ayin cewa a daina biyan kuɗin fansa in ya so ɓarayin su yi ta kashe waɗanda sukan kama har sai sun gaji su daina don ba kuɗi ba zai zama mafita guda ɗaya ba. Babban varawon da ya sace ɗaliban jami’ar Greenfield a Kaduna Sani Idris Jalingo da a ka fi sani da Ɓaleri, ya ce duk wanda ya samu kan sa a hannun su to zai iya sauya matsayar cewa kar a ba da kuɗin fansar. Ɓaleri ya ce ko Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru Elrufai ne da ke kan gaba wajen yaƙi da batun ba da kuɗin fansa; ya faɗa hannun su, zai buƙaci a biya ko nawa don ya samu kuvuta saboda yanayin tashin hankalin da wanda a ka sace ya kan shiga.

Masu sharhi na ba da shawarar a haɗa dukkan matakan na magance wannan babbar annoba da suka haɗa da sulhu da masu sauƙin kai da za su iya tuba ba irin na muzuru ba. Biyan diyyar wasu masu ƙorafi a tsakanin miyagun musamman waɗanda a ka sacewa dubban shanu da kuma dirar mikiya kan waɗanda suka zama shaiɗanu masu taurin kai a cikin su. Tsarin shi ne amfani da ’yan gari a harkar wajen magance sauran waɗanda ba su da niyyar ajiye makamai.

Kazalika ya dace a duba gaskiyar jami’an tsaro da ke kula da waɗannan yankuna da a ke samun wannan ƙalubale da kuma amfani da dazukan wajen buɗe gonaki, filayen kiwo ta hanyar dawo da burtali na dauri a inda hakan zai yiwu.

Abu na ƙarshe shi ne, ɗaukar masu sintiri a dazuka da za a ba su horon samar da bayanai don ɗaukar mataki gabanin aukuwar duk wani akasi. Shin wace rana ce mutum zai bi hanyar garin su a Arewa ba tare da ɓalli-ɓallin sa ya tashi ba don fargabar za a iya sace shi?