Daga BASHIR ISAH
Babban Lauyan Nijeriya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya tabbatar cewa Gwamnatin Tarayya ta karɓi maƙudan kuɗaɗe Fan milyan £4,214,017.66 na kuɗaɗen sata da aka danganta su da iyalan tsohon Gwamnan Jihar Delta, James Ibori.
Mai taimaka wa ministan kan sha’anin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Umar Gwandu, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja a ranar Talata.
Bayanan Gwandu sun nuna an rigaya an saka kuɗaɗen a kwatankwacin Naira cikin asusun Gwamnantin Tarayya tun a 10 ga Mayu, 2021.
Haka nan cewa Minista Malami ya rattaba hannu a takardar yarjejeniyar karɓar kuɗaɗen da Ibori ya wawushe a madadin Gwamnatin Nijeriya.
A cewar Malami, wannan wani tagomashi ne da Nijeriya ta samu albarkacin himmar da ta nuna wajen ƙwato kuɗaɗen gwamnati da aka sace waɗanda aka samar don yi wa ƙasa aiki da su.
