Tarwatsa zanga-zanga: ’Yan daba sun maye gurbin ’yan sanda

*A baya jami’an tsaro ake zargin da kawo cikas
*Yanzu ’yan daba sun hutasshe su
*Shin ko bambancin salon mulkin APC da na PDP ne?
*Yadda fusatattun matasa suka kai wa NLC hari a Kaduna

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

A Nijeriya lokutan gudanar da zanga-zangar nuna ƙin jinin gwamnati ko adawa da wani mataki da ta ɗauka an saba ganin yadda ta ke amfani da jami’an tsaro na ’yan sanda wajen tarwatsa masu zanga-zanga, inda ake zargin su da yin amfani da hayaƙi mai sa hawaye, motar ruwan zafi, kulake, wani lokacin ma har da harsashin bindiga ko makamatansu, don kawo cikas ga yiwuwa ko ɗorewar zanga-zangar.

To, amma a ’yan shekarun baya-bayan nan lamarin ya sauya salo, inda maimakon ’yan sanda su riƙa fitowa suna yin fito-na-fito da masu gudanar da zanga-zanga, a yanzu ’yan daba ko wasu ɓatagari ne bayyana tamkar iskokai suna afka wa duk wanda ya fito zanga-zanga da sunan nuna ƙin jinin gwamnatoci ko wasu manufofinsu a matakai daban-daban.

Irin wannan tashin-tashina ta baya-bayan nan ita ce wacce ta faru a Jihar Kaduna, inda a lokacin ga Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ke gudanar da zanga-zangar lumana, don nuna a dawa da yadda gwamnatin jihar ta kori ɗimbin ma’aikata daga aiki, sai katsam irin waɗancan ɓatagari ko ’yan daba suka yi musu dirar mikiya, suka tarwatsa su, inda lamarin nan take ya koma na zubar da jini da tashin hankali.

Tun ma kafin zuwan wannan Jamhuriya ta Huɗu, a lokutan mulkin soja an sha yin artabu da tsakanin jami’an ’yan sanda da mambobin ƙungiyoyin farar hula daban-daban. Ba NLC ce kaɗai ke samun irin wannan arangama ba, hatta ƙungiyar ɗalibai ta taɓa yin arangama da ’yan sanda a Legas lokacin mulkin soja na Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB). Su ma ƙungiyoyin siyasa da na yankuna sun sha artabu da jami’an tsaro a lokacin mulkin gwamnatin soja ta Marigayi Janar Sani Abacha.

Bayan kafuwar Jamhuriya ta Huɗu a ƙarƙashin gwamnatocin Cif Olusegun Obasanjo da Umaru Musa Yar’Adua da kuma Goodluck Ebele Jonathan an sha samun arangamar yunƙurin daƙile zanga-zanga da ’yan sanda ke yi, inda ake zargin su da cin zarafin masu gudanar da jerin gwano suna fakewa da cewa, za su haifar da tashin hankali.

To, amma tun bayan zuwan Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a 2015 zuwa yanzu, zargin da ake yi wa ’yan sanda ya yi matuƙar raguwa. A taƙaice ma dai, ko lokacin da aka yi shahararriyar zanga-zangar nan ta #EndSARS, ba a ƙarfafa zargi kan ’yan sanda ba, domin a Jihar Legas, sojoji aka zarga da aikata kisan kiyashi, wanda shi ma a ƙarshe an kasa mayar da labarin ba na ƙanzon kugere ba.

Ko a biranen Abuja, Kano da Legas da aka bayar da rahotannin artabun tarwatsa masu zanga-zangar, abin da rahotanni suka tabbatar shine, wasu ’yan adaba ne suka yi wannan aika-aika, kamar yadda ya faru a Kaduna kwanan nan.

Hatta a lokutan zaɓuka, sai dai a ji labarin cewa, wasu waɗanda ba a san ko su waye ba, sun afka wa masu kaɗa ƙuri’a ko sun tayar da tarzoma, kamar yadda aka yi zargin hakan a Babban Zaɓen Jihar Kogi da kuma zaɓen cike giɓin kujerar gwamna da aka a gudanar a Mazaɓar Gama da ke Kano, zaɓen da ya janyo cece-kuce a 2019.

Babban abin tambaya a nan shine, shin mene ne dalilin da ya kawo irin wannan sauyi tun bayan kafuwar gwamnatin APC? Haƙiƙa za a iya danganta lamarin wasu dalilai da ke alaƙa da sauye-sauye da kuma taka-tsantsan na dabarun siyasa da hangen gaba.

A yanzu duniya ta zama tamkar ɗaki guda ta yadda duk abin da ke faruwa yana kan idanu kowa. Sojoji da sauran jami’an tsaron da suka aikata ta’annati a lokutan zanga-zanga suna iya fuskantar shari’a a Kotun Duniya bayan sun yi ritaya. Bugu da ƙari, tsoma hannun jami’an tsaro kai-tsaye a irin wannan zanga-zanga yana sanya wa gwamnati matu}ar ba}in jini da ya ke sanya ta ƙara samun matuƙar ƙalubale.

A cikin shekara ta 2012 an samu artabu tsakanin ’yan sanda da masu zanga-zangar ƙalubalantar dawo da tallafin mai a faɗin Nijeriya, inda ake ganin amfani da yaji mai sa hawaye (tiyagas) da jami’an tsaro suka yi a Kano ya taka rawa wajen rasuwar tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Chuba Okadigbo. Masu nazari na ganin cewa, hakan ba komai ya ƙara wa gwamnatin Jonathan ba, illa matsin lamba da kuma share fage wajen faɗuwar gwamnatinsa a Babban Zaɓen 2015 ƙarƙashin tutar PDP.

Bisa la’akari da ire-iren hakan, za a iya cewa, ’yan siyasar gwamnatin APC kenan sun zo da sabon salo ko sabuwar dabara ta nesanta kansu da aikata irin wannan masha’a. To, amma fa ba za a kasa danganta su da wannan matsala ba, idan aka lura da cewa, jami’an tsaro ba su cika kamawa da gurfanar masu tarwatsa zanga-zangar ko mayar da ita tashin hankali ba, illa dai kawai su kan fake da hakan wajen haramta sake fitowa zanga-zanga ko cigaba da yin ta.

Abin duba a nan shine, gano jami’an da suka yi ta’annati a lokacin gudanar da bincike, ya fi gano ’yan dabar gari sauƙi.