Buhari da ziyarar sa a ƙasar Faransa

A kwanaki kaɗan da suka gabata, wato ranar 16 ga Mayu, 2021, ne, Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya buga bulaguro zuwa Birnin Paris, babban birnin Ƙasar Faransa, inda Shugaban ƙasar ta Faransa, Emmanuel Macron, ya karɓi baƙuncin shugabannin ƙasashen Afrika a taron tattaunawa kan jikkatar da aka sha sakamakon ɓarkewar annobar Cutar Korona da kuma duba yiwuwar samun tallafi, musamman bisa irin bashin da ya yi wa ƙasashen na Afrika katutu, sannan kuma ya ke ci gaba da ƙaruwa.

Sai dai kuma, a sanarwar da Fadar Shugaban Nijeriya da ke Abuja ta bayar mai ɗauke da sa hannun Babban Mai Taimaka wa Shugaban ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai, Malam Garba Shehu, gabanin tafiyar Shugaba Buharin a ranar 15 ga Mayu, 2021, fadar ta ce, Shugaba Buharin zai kuma yi ganawar musamman da Shugaba Macron kan barazanar tsaro da ke addabar yankin Sahel da Tafkin Chadi a Afrika ta Yamma da kewaye.

Kana, za su kuma tattauna kan dangantakar siyasa, tattalin arziki, canjin yanayi da kuma ha]in gwiwa kan sashen lafiya, musamman yunƙurin daƙile yaɗuwar annobar Korona ta hanyar ƙara azama wajen gudanar da bincike da kuma rigakafin cutar. Haka nan Shugaba Buhari zai gana da masu ruwa da tsaki kan harkokin kasuwanci, iskar gas da sauran harkokin tattalin arzikin a birnin na Paris.

Haƙiƙa wa]annan bayanai sun nuna cewa, idan Shugaba Buhari ya yi amfani da wannan bulaguro yadda ya kamata, tabbas Nijeriya da ’yan ƙasarta za su yi matuƙar amfana da tafiyar, domin a yanzu babu abin da ya fi addabar ’yan ƙasar kamar batun tsaro da kuma ƙangin talauci. Don haka duk wani motsi da gwamnati za ta yi. zai fi amfanarwa ne idan kawai ta mayar da hankali wajen shawo kan wa]annan matsaloli, musamman ma a Arewacin ƙasar.

Ziyarar da kuma ganawar musamman da Macron, sun gwada cewa, Gwamnatin Shugaba Buhari ta na sane da halin da ’yan Nijeriya ke ciki kuma tana tagazawa wajen ganin ta share musu hawaye. Kodayake masu iya magana suna cewa, idan dambu ya yi yawa, ba ya jin mai, amma shugabanni na gari ba sa saurarawa a ƙoƙarinsu na ganin sun warware manyan matsalolin da ke addabar al’ummarsu ta hanyoyi daban-daban, inda kuma za a iya cewa, irin wannan ziyara da Shugaba Buhari ke yi na daga cikin kyakkyawan misalin hakan.

A irin wannan lokaci, ɗan Nijeriya, musamman ma ]an Arewa, babu abin da ya fi damun sa irin ya ga kwanciyar hankali da lumana da kuma yalwar arziki sun dawo masa; abubuwan da ya rasa tun shekaru da dama kafin zuwan wannan gwamnati.

A fili ta ke cewa, Gwamnatin Tarayya ta fitar da maƙudan kuɗaɗe; kimanin malala gashin tunkiya, don shawo kan matsalar tsaro da talauci a faɗin ƙasar, amma da alama har yanzu an kasa ganin abin da zai ture wa buzu naɗi. Ko da ba a faɗa ba, wannan kuwa ya faru ne sakamakon yadda takidin masu zagon ƙasa ke yin matuƙar tasiri wajen daƙile duk wani yunƙuri ko ƙoƙari da gwamnatin ke yi na ganin an fitar da jaki daga cikin duma.

To, amma a yanzu, idan aka yi la’akari da neman ha]in kan da Shugaba Buhari da gwamnatinsa ke yi daga ƙasashe irin su Faransa, musamman a wannan ziyara da ya kai Paris, za a iya cewa, an ɗauko hanyar hawa tudun-mun-tsira.

Babban abin dubawa shine, ita Nijeriya ƙasa ce, wacce ta ke da maƙotaka da ƙasashe rainon Faransa. Wato ƙasashen da suka haɗa da Nijar, Kamaru da Chadi. Su kuwa waɗannan ƙasashe na rainon Faransa har yanzu ƙasar tana da tasiri akansu ta kusan kowacce irin fuska da suka ha]a da tsaro, tattalin arziki, siyasa ko shugabanci da sauransu.

Don haka idan Nijeriya ta haɗa kai da uwa-ma-bada-mamansu, za a iya samun wata nasara, wacce a yanzu ba za a iya ƙiyasta ta ba, domin a cikin irin abubuwan da wasu masu nazari ke kallo a matsayin dalilan kasa shawo kan matsalolin Nijeriya, akwai tasirin maƙotanta a ciki.

Rahotanni sun sha nuna yadda ake zargin cewa, ’yan ta’adda suna fakewa a maƙotan ƙasashe bayan sun kawo hari ciki ko iyakokin Nijeriya ko kuma suna iya zama a can suna shirya yadda za su kitsa kai hare-hare a cikin Nijeriya.

Daina samun irin wannan mafaka, zai taimaki Nijeriya wajen shawo kan matsalar tsaro, amma ana ganin cewa, sai ƙasar Faransa ta tallafa wajen zare wa rainon nata idanu.

Bugu da ƙari, akwai bayanai masu inganci da ke nuni da cewa, ana amfani da ƙasashe masu maƙwabtaka da Nijeriya wajen safarar miyagun makamai, inda ƙarancin sa ido daga gare su, ke haifar da shiga da makamai Nijeriya. Shi ma wannan zai iya samun lahani, idan Faransa ta murza gashin baki.

Ta fuskar fatara da talauci da ke addabar ɗan Nijeriya, musamman a Arewa da Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana jihohinta a matsayin mafiya talauci, kuwa, ana ganin cewa, Faransa za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen tayar da komaɗar tattalin arzikin Nijeriya da talakan ƙasar, musamman don kasancewar Faransa mai ƙarfin tattalin arziki kuma mai faɗa-a-aji a duniya.

Da wannan kaɗai, za a iya cewa wannan tafiya ta Shugaba Buhari zuwa Birnin Paris, Alla ya idda nufi! Sam-barka!!!