Ƙaramar Sallah: Buhari ya nemi a yi ‘Alƙunutu’

*Ɗahiru Bauchi ya ƙalubalanci Sarkin Musulmi
*Tinubu ya nemi a yi wa Buhari addu’a
*Saraki ya yi nasiha

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

A jiya Alihamis ne a Nijeriya da ma yawancin ƙasashen duniya aka gudanar da bikin ƙaramar Sallah ta bana, 13 ga Mayu, 2021 na shekarar Masihiyya, wacce ta zo daidai da 1 ga Shawwal, 1442 bayan Hijira, inda Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya buƙaci ’yan Nijeriya da su gudanar da addu’o’in maganta ayyukan ’yan ta’adda da kuma masu neman mulki ko ta halin ƙaƙa.

Sallar idin kuma ta zo ne a daidai lokacin da fitaccen malamin addinin Islama kuma jagoran a Ɗariƙar Tijjaniyya, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, ya ƙalubalancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, wanda ya bayar da umarnin cika azumin watan Ramadan zuwa 30 tare da gudanar da Sallar Idi jiya, Alhamis.

Shi kuwa tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma Jagoran Jam’iyya mai mulkin Nijeriya, Alhaji Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, a saƙonsa na ranar sallar, kira ya yi da a yi wa Shugaba Buhari addu’o’in samun nasarar shawo kan matsalolin da ke addabar ƙasar.

A daidai lokacin ne kuma, tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Bukola Abubakar Saraki, ya yi nasiha ga ’yan Nijeriya bayan kammala azumin na Ramadan, inda ya buƙaci a ci gaba da ɗabbaƙa kyawawan halayen da aka koya a cikinsa.

Su ma shugabannin Majalisar Dokoki ta ƙasa, Sanata Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila, sun aike da nasu saƙonnin barka da sallar ne, don taya al’ummar Musulmi bikin nata.

Saƙon sallah: A yi wa ’yan ta’adda da masu neman mulki ido-rufe alƙunutu – Buhari

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya yi kira ga ’yan ƙasar da su yi addu’ar kawo ƙarshen masu aikata ta’addanci da kuma waɗanda neman mulki ya rufe musu idanu har suke neman rikita zamantakewar Nijeriya da ha]in kanta, don kawo ƙarshen mugun nufinsu.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a cikin saƙonsa na ranar ƙaramar Sallah mai ɗauke da sa hannunsa, inda kuma Mai Magana da Yawunsa, Malam Garba Shehu, ya raba wa manema labarai a Abuja, biyo bayan kammala azumin watan Ramadana, inda aka gudanar da Sallar Idi jiya.

“Ya kamata mu hannu wajen yin addu’a ga masu satar mutane da yin garkuwa da kuma kashe-kashe, sannan da waɗanda idanunsu ya rufe wajen neman mulki ti ta halin ƙaƙa, inda suke yin faman yin ɓatanci da barazana ga ha]in kan ƙasa da ma wanzuwarta a matsayin ƙasa guda,” inji shi.

Daga nan sai shugaban ya yi kira ga malamai, sarakuna da ’yan siyasa da su mayar da hankali wajen ƙarfafa wa ’yan ƙasa gwiwar nuna ƙauna ga junansu, yana mai kira da aka ankara da halayen waɗanda ke son yin amfani da bambancin addini wajen tayar da zaune tsaye, don buƙatar ƙashin kansu.


Ɗahiru Bauchi ya ƙalubalanci Sarkin Musulmi kan ganin watan Shawwal

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya samu ƙalubale daga jagoran Ɗariƙar Tijjaniyya, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, dangane da ganin watan Shawwal na wannan shekara ta 1442 na Hijirar Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wassallam.

Ranar Talata, 29 ga watan Sharu Ramadan, wanda ya yi daidai da shekarar Masihiyyah, 11 ga Mayu, 2021, Kwamitin Bayar da Shawara kan Addinin Musulunci da ke ƙarƙashin Majalisar Addinin Musulunci ta ƙasa, wacce Sarkin Musulmin ke jagoranta, ya bayyana cewar, bai samu labarin ganin watan Shawwal ba.

Ɗahiru Bauchi

Bisa wannan dalili, kwamitin a ƙarƙashin jagorancin Wazirin Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya bayyana cewar, Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar ya amince da wannan rahoto nasa. Don haka ya ayyana ranar Alhamis 13 ga Mayu a matsayin ]1 ga Shawwal, 1442 (AH), wacce ta yi daidai da ranar ƙaramar Sallah.

Amma a daidai wannan rana ta Talata, 29 ga Sharu Ramadan, wanda ya yi daidai da ranar 11 ga Mayu, 2021, ita kuma wasu mabiyan Sheikh Bauchi a garin Bauchi suka yi tutiyar ganin watan Shawwal, inda suka ayyana washegari Laraba ce a matsayi 1 ga Shawwal.

Babban jagora na ɗariƙar, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, wanda ya tabbatar da ganin watan na Shawwal, da wasu almajiransa da ke garin na Bauchi suka gani, sai ya bayar da umarni a sha ruwa ranar Laraba, 12 ga Mayu, 2021, tare dayin Sallar Idi a ranar a matsayin ɗaya ga watan Shawwal 1442 (AH).

Sheikh Bauchi ya umarci babban ɗansa, Ahmad Tijjani Dahiru Bauchi, ne ya jagoranci sallar ta idin mai raka’o’i biyu tare da yin huɗuba, wanda dubban magoya baya suka halarta a farfajiyar gidan malamin da ke garin Bauchi.

Da yake ganawa da manema labarai bayan gabatar da sallar idi, shehin malamin, Sheikh Ɗahiru Bauchi, ya bayyana cewar, sun ajiye azumin Ramadan ne bayan sun tabbatar da ganin watan Shawwal daga adalan mutane.


Saƙon barka da sallah: Saraki ya yi wa ’yan Nijeriya nasiha

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ta Nijeriya, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya taya ɗaukacin al’ummar Musulmin Nijeriya murnar kammala azumin Ramadana na wannan shekara ta 2021, tare kuma da yi musu barka da sallah.

Saraki a wata takardar manema labarai, mai ɗauke da sa hannun shugaban sashen ofishin watsa labaransa, Yusuph Olaniyonu ya shawarci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da neman kusanci ga Allah tare da yin addu’ar samuwar mafita ga Nijeriya.

Saraki

Ya ƙara da cewa, watan azumin Ramadana ba kawai ya ta}aita ga kyautata halaye na tsawon kwanaki 30 ba ne, lokaci ne da ya kamata mu sauya halayenmu zuwa masu nagarta.

Ya ce: “Ya kamata mu yi bankwana da duk wasu munanan ɗabi’u da muke da su kafin zuwan Ramadan, mu zama managarta kuma masu kishin kasa wadanda ke yi wa ƙasa addu’a a kodayaushe, don a samu hadin kai, adalci da zaman lafiya.

“Halin da kasarmu Nijeriya ke ciki na bukatar kowannenmu ya canza kansa. Mu yi amfani da darussan da muka koyo daga makarantar Ramadana wurin yin watsi da duk wata ɗabi’a da muka san ba ta kirki ba ce. Nijeriya ta fi buƙatar addu’o’inmu a irin wannan lokaci fiye da koyaushe.

“Bisa la’akari da rashin tsaro da ake fama da shi da kuma yawaitar talauci, dole ne mu hada kai wurin nuna kishin kasa don tsamo Nijeriya daga halin da take ciki,” inji shi

Daga ƙarshe Dr. Saraki ya yi addu’a ta musamman ga jami’an tsaro, musamman waɗanda ke bakin fama, don bayar da kariya ga Nijeriya. Ya yi addu’ar Allah Ya ci gaba da ba su nasara a yakin da suke yi da ‘yan ta’adda.

Ya ƙara da cewa, watan azumin Ramadana ba kawai ya taƙaita ga kyautata halaye na tsawon kwanaki 30 ba ne, lokaci ne da ya kamata mu sauya halayen mu zuwa masu nagarta.

Ya ce: “Ya kamata mu yi bankwana da duk wasu munanan ɗabi’u da mu ke da su kafin zuwan Ramadan, mu zama managarta kuma ma su kishin ƙasa waɗanda ke yi wa ƙasa addu’a a ko da yaushe, don a samu ha]in kai, adalci da zaman lafiya.

“Halin da kasar mu Nijeriya ke ciki na buƙatar kowannen mu ya canza kan sa. Mu yi amfani da darussan da mu ka koyo daga makarantar Ramadana wurin yin watsi da duk wata ɗabi’a da mu ka san ba ta kirki ba ce. Nijeriya ta fi buƙatar addu’o’in mu a irin wannan lokaci fiye da ko yaushe.

“Bisa la’akari da rashin tsaro da ake fama da shi da kuma yawaitar talauci, dole ne mu haɗa kai wurin nuna kishin ƙasa don tsamo Nijeriya daga halin da ta ke ciki.” Inji shi

Daga ƙarshe Dr. Bukola Saraki ya yi addu’a ta musamman ga jami’an tsaro, musamman waɗanda ke bakin fama don bayar da kariya ga Nijeriya. Ya yi addu’ar Allah Ya ci gaba da ba su nasara a yaƙin da su ke yi da ‘yan ta’adda.


Saƙon barka da sallah: Tinubu ya nemi ‘yan Nijeriya da su yi wa Buhari addu’a

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jagoran jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya, Cif Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su ajiye siyasa su yi wa Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ƙasa addu’ar samun zaman lafiya.

Tinubu

Bola Tinubu ya ce kalaman wasu ‘yan siyasan ya fita daga cikin tsari na adawa, sai dai ƙin gaskiya da kuma cin amanar ƙasa. Ya ce ka da mutane su biye wa gurɓatattun ‘yan siyasan da su ba ƙasar ba ce a gaban su.

“Ka da mu yi la’akari da kalaman wasu ɓata garin ‘yan siyasa da su ke yi a kan Shugaba Buhari, kamata ya yi mu duƙufa wajen yi mishi addu’a don ganin cewa Nijeriya ta samu tabbataccen zaman lafiya da yalwar arziki a ƙasa.

A cikin saƙon nasa na barka da sallah, Tinubu ya ci gaba da cewa “Mu tuna da Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatin sa a cikin addu’o’in mu don su samu ƙarfin da ake buƙata da hikima wajen kare al’umma, tare da tunkarar ƙalubalen tsaron da ke addabar ƙasar mu, da kuma taimakawa don bunƙasar Nijeriya,” inji shi.