Zarcewa da ayyukan alheri har bayan Ramadan

Kamar yau aka fara azumin watan Ramadana ranar 13 ga Afrilu, 2021, wanda ya zo daidai da 1 ga Ramadan, 1442, ga shi a shekaranjiya Laraba, 13 ga Mayu, 2021, wanda ya zo daidai da 30 ga Ramadan, 1442, an kammala azumin, kuma a jiya Alhamis aka gudanar da Sallah Ƙarama, wato ranar 1 ga Shawwal, 1442, kenan. Wannan ya gwada irin izinar da rayuwa ke da ita ta cewa, kullum ran mutum yana ƙarewa cikin hanzari ne.

A lokacin da muke yi muku maraba da shigowar watan azumin Ramadana mai taken ‘Yayin da watan Azumi ya }arato’, a shafin Ra’ayinmu na ranar 9 ga Afilu, 2021, wanda ya zo daidai da 27 ga Sha’aban, 1442, mun bayyana ra’ayi kamar haka;

“A makon da za mu shiga ne ake sa ran ɗaukar azumin watan Ramadan, wata mai alfarma ga dukkan Musulmin duniya. A ranakun wannan wata, waɗanda suke kamawa guda 29 ko 30 a kowacce shekara, Musulmi sukan kaɗaita daga aikata wasu muhimman abubuwa a rayuwar ɗan adam da rana, kamar ci, sha da jima’i. Lokacin haramcin hakan yana kamawa ne daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana a kulliyaumin.

“To, a zahirin gaskiya ba waɗannan abubuwa ne kaɗai abubuwan da ake sa ran Musulmi ya guje su ba, illa dai kawai za a iya cewa, waɗannan abubuwa guda uku, wato ci, sha da jima’i, sun kasance wani ma’auni da zai zama abin gwaji ga halayya da ɗabi’un ɗan adam ta fuskar nuna juriya, dauriya, haƙuri da kuma yakana.

“Abin nufi a nan shine, muddin mutum zai iya kauce idanunsa daga ci, sha da kuma saduwa, to ana sa ran zai iya kauce wa dukkan wani abu zuciyarsa za ta iya raya masa cewa, tana buƙatar sa, domin ba kasafai ɗan adam ke cin karo da abinda ya zarce buƙatar wa]ancan abubuwa uku ba. To, idan har zai iya barin su, duk da cewa, ana kallon su tamkar tilashi, to lallai kenan zai iya barin wani abu saɓanin hakan kenan.

“A taƙaice dai, idan har mutum zai iya ƙaurace wa ci, sha da saduwar aure, to kenan zai iya kauce wa ɗabi’a ta ƙeta, gulma, cin hanci da rashawa, cin amana, ƙazafi, ƙarya, sata, fashi, ta’addanci da dukkan wani abin ƙi da ake ji ko gani. Don haka, duba da wannan, haƙiƙa za a iya cewa, akwai matuƙar ɗimbin hikima a sha’anin umarnin da aka bayar ga Musulmi na ibadar watan Azumi na Ramadana.

“Muhimmin abinda ya kamata ɗan adam ya lura da shi kan wannan hikima ta Allah (SWT) na umartar bayinsa da su azumci watan Ramadan shine, ashe za su iya kauce wa dukkan wani abu da yake na ƙi ba tare da sun rasa komai a rayuwarsu ba. A taƙaice ma dai, guje wa abin ƙi, fa’ida ce da shi, domin ga abbubuwan da ba na ƙi ba ne ba ma, amma sun zamo wasu abubuwa masu alheri. Wato ƙaurace wa ci, sha da jima’i ya koyar da kai wani abu mai amfani a rayuwarka ta fuskar ɗabi’a. Bugu da ƙari, hatta likitoci sun tabbatar da cewa, azumi yana inganta lafiyar jikin ɗan adam.

“Tabbas da mutane a jimlace za su yi aiki da hikimar da ke cikin azumtar watan Ramadan, da rayuwa ta yi sauƙaƙa. Hatta cin hanci da rashawa da ake ganin sun yi katutu a ma’aikatun gwamnati za su iya zama tarihi. Hatta cin amana da ake ganin sun yi katutu a tsakanin jama’a, za su iya zama abubuwan tunawa kawai watarana. Hatta matsalolin auratayya da ake ganin su ma sun yi katutu a cikin al’umma za su iya wucewa.

“Don haka ba hana ka cin abinci ko shan abin sha ko kusantar mata ne kaɗai abin la’akari a lokacin wannan wata mai alfarma ne abin dubawa kaɗai ba, a’a, yana da kyau a fahimci hikimar da ke ciki, sahihiyar hikima kuwa. Fa’idar da ke cikin wannan kuwa za ta iya haɗa wa har ga wanda ma ba Muslmin ba ne, domin ita nagarta kowa yana iya aikata ta, imani kuma wani abu ne daban.

“Bugu da ƙari, kasancewar malamai sun tabbatar mana da cewa, a cikin watan Azumin Ramadana akwai wata sa’a ta amsa addu’o’in bayi da Allah (SWT) Ya kaɗaice, Ya ware ta gare su, don amsa dukkan abinda suka roƙe shi, to yana da matu}ar muhimmanci al’ummar Musulmi su sanya ƙasarsu a cikin addu’o’insu, saboda halin da Nijeriya ta tsinci kanta a ciki na matsalolin da suka dabaibaye ta. Haka nan su ma shugabanni, waɗanda Allah Ya ɗora wa alhakin tafiyar da ragamar mulkin ƙasar, suna buƙatar a sanya su a cikin addu’o’i. Kada mu manta da cewa, nagartar shugaba ita ce, kyautata rayuwar waɗanda ya ke shugabanta. Saboda mu na buƙatar mu sanya a cikin addu’o’inmu, domin su samu damar kyautatawa da inganta rayuwarmu.

“Mu na roƙon Allah Ya amsa ibadarmu kuma ya ji roƙonmu. Allah ya sa wannan wata mai alfarma ya zamo silar shiryarmu da fitar da mu daga cikin dukkan wani ƙunci da ke damun mu bakiɗaya. Amin summa amin!”

Wannan ra’ayi namu ba komai ya ke nufi ba, illa ɗorewa kan tafarkin ayyukan alheri. Don haka kawo ƙarshen azumin Ramadan ba ya nufin kawo ƙarshen ayyukanmu na alheri. Yana nufin ashe za mu iya jurewa da ɗorewa kan nagarta kenan, tunda idan har za mu iya kwashe wata guda, wato kwanaki 30 cur muna kwatanta ayyukan alheri ka’inda’na’in!

Allah ya ba mu ikon ɗorewa da dauwama kan tafarkin alheri. Barka da sallah!