Bikin Sallah: Buhari ya buƙaci a kiyaye dokokin korona, ya soke gaisuwar sallah

Daga UMAR M. GOMBE

Shugaba Muhammadu Buhari ya kira ga ‘yan Nijeriya da a kula tare da lura a lokacin bikin ƙaramar sallah na bana duba da cewa har yanzu annobar korona na ci gaba da yi wa duniya barazana.

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu, ya ce a bisa dalilai na annobar korona ya sa a bana Shugaba Buhari tare da iyalansa da manyan jami’an gwamnatinsa za su gudanar da sallar Idi a cikin Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, suna masu kiyaye dokikin da aka shata din yaƙi da cutar korona.

Sanarwar da Garba Shehu ya fitar a madadin Shugaban Ƙasa, ta nuna Shugaba Buhari ya soke gaisuwar sallah wadda shugabannin addinai da na al’umma da ma na siyasa suka saba kai wa Shugaban Kasa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito Shugaba Buhari ya ui amfani da wannan dama wajen miƙa godiyarsa ga shugabannin addinai da suka bada gudunmawarsu wajen yi wa ƙasa da al’ummarta addu’o’i na fatan alheri.

Kazalika, Buhari ya sake amfani da wannan dama wajen miƙa ta’aziyyarsa ga waɗanda suka yi rashin ’yan’uwansu sakamakon rikice-rikicen da suka riƙa faruwa a sassan ƙasa.

Tare da yin kira ga shugabannin al’ummomi da su gargaɗi matasansu dangane da haɗarin da ke tattare da batun tada zaune tsye a cikin ƙasa.