Hoto: Mako guda da kammalawa, gadar da gwamnatin Kogi ta gina ta ɓurma

Kimanin mako guda kenan da kammala gina gadar Ozuma da ke yankin Okene ƙarƙashin Gwamnatin Yahaya Bello, amma sai ga shi gadar ta karye a daidai lokacin da wata babbar mota ke ƙoƙarin wucewa. Wata majiya mai tushe ta ce da alamu injiniyoyin da suka yi aikin gina gadar sun yi amfani da ƙarafan da ƙwarinsu bai kai yadda ya kamata ba wajen gina gadar.