Hajjin bana: Muna jiran tabbaci daga bakin Saudiyya – NAHCON

Daga WAKILINMU

Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta bayyana jin daɗin ta game da bayanin da ya fito daga ƙasar Saudiyya cewa za a yi aikin Hajjin bana, tare da cewa bayanin wani albishir ne gare ta da ma al’ummar Musulmin duniya baki ɗaya.

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Babbar Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta hukumar, Hajiya Fatima Sanda Usara, NAHCON ta bayyana cewa, duk da dai Saudiyya ba ta ambata cewa ko ƙasashen duniya za su yi aikin Hajjin na bana ba a taƙaitacciyar sanarwar da ta fitar ranar Lahadi, hukumar na fatan cewa Hadimin Masallatan Harami Biyu zai bada damar ƙasashen duniya su je aikin Hajjin na 2021.

Usara ta ce a yayin da hukumar ke dakon ƙarin bayani a kan tsare-tsaren da za a yi na Hajjin bana daga Ma’aikatar Harkokin Hajji da Ummara ta Saudiyya, NAHCON na kira ga maniyyatan Nijeriya da su ci gaba da haƙuri su kuma ƙara dagewa da addu’a domin a ji bayani mai ƙarfafa gwiwa.

Ta ce, “In dai akwai tsarin da zai bai wa ‘yaan ƙasashen waje su je aikin Hajjin na bana, to NAHCON na da yaƙinin cewa maniyyatan Nijeriya za su samu kujeru ko da kuwa da sharuɗɗa ne. Hakan zai faru ne saboda a halin da ake ciki, ‘yan Nijeriya na cikin ƙasashen da aka bai wa damar zuwa Umura kuma Nijeriya ba ta cikin ƙasashen da aka hana zuwa Saudi Arebiya.

“Saboda haka, NAHCON na tabbatar wa ‘yan ƙasa, musamman ma waɗanda aka yi wa rijistar zuwa Hajjin bana cewa za ta yi biyayya ga duk wani tsari, sharaɗi da shiri da Ma’aikatar Harkokin Hajji da Umura ta Saudiyya ta gindaya.

“Don haka NAHCON na kira ga masu ruwa da tsaki da maniyyata da suma su ɗauri aniyar yin biyayya da tsare-tsaren domin sauƙaƙa wa Nijeriya da Saudiyya wajen cim ma nasarar shirin Hajjin na bana duk da mawuyacin halin da ake ciki.”