Haɗarin jirgin ruwa ya ci mutum 28 a Neja

Daga AISHA ASAS

A ƙalla mutum 28 ne aka ruwaito sun mutu a wani haɗarin jirgin ruwa da ya auku a yankin ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Darakta Janar na Hukumar Bada Agajin Gaggawa na Jihar, Ahmed Inga ne ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) da aukuwar hakan a Minna, a Lahadin da ta gabata.

A cewar Inga, fasinjojin da lamarin ya rutsa da su sun fito ne daga Zumba da nufin zuwa ƙauyen Tija a yankin ƙaramar hukumar Munya da ke jihar.

Ya ci gaba da cewa haɗarin ya auku ne da yammacin Asabar da ta gabata da misalin ƙarfe 6 bayan da ya rage tazarar mita 50 su kai inda za su tsaya, inda jirgin nasu ya daki wani kututtiren itace da ke ƙarƙashin ruwa sannan ya karye nan take.

Ya ce mutum 65 ne suka tsira da ransu a haɗarin yayin da aka gano gawarwakin mutum 28, sannan ana kan binciken wasu mutum 7 da suka ɓace.