Gwamnati ta bada hutun kwana biyu albarkacin bikin sallah

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta bayyana Laraba 12 da Alhamis 13 ga Mayu, 2021, a matsayin ranakun hutu na gama-gari domin bikin ƙaramar sallah na bana.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, shi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a Abuja a madadin Gwamnantin Tarayya.

Aregbesola ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga Musulmi ‘yan Nijeriya na gida da ƙetare, da su yi amfani da wannan dama wajen yi wa Nijeriya addu’ar samun zaman lafiya mai ɗorewa da daidaiton tattalin arzikin ƙasa yayin bikin na Idul Fitr.

Ministan ya ce babu yadda za a yi ƙasa ta samu cigaba ba tare da zaman lafiya ba, don haka ya buƙaci ɗaukacin ‘yan Nijeriya da su zamo masu biyayya ga doka da oda, son juna da haƙurin zama tare kamar dai yadda Annabi Muhammad (SAW) ya karantar.

Kazalika, ya yi kira ga hukumomin tsaro na faɗin ƙasa da su matse ƙaimi wajen ci gaba da yaƙi da matsalar ta’addanci da sauran matsalolin tsaron da suka addabi ƙasa domin kawo ƙarshe masu aikata muggan laifuka a cikin ƙasa.

Haka nan, ya bada tabbacin cewa Gwamnatin Buhari na yin dukkan mai yiwuwa don cika ƙudirinta na son ganin zaman lumana ya dawo a sassan ƙasa yadda ya kamata.

Ya ce, “Wannan gwamnatin ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai ta tabbatar da cewa al’ummar ƙasa kowa na iya zirga-zirga hankali kwance ba tare da wani tsoro ko fargaba ba ga rayuwarsa da dukiyarsa.”

Daga nan Minista Aregbesola ya yi amfani da wannan dama wajen taya al’ummar Musulmi murna da kuma fatan a yi bikin Idul Fitr lami lafiya.