Babban Labari

Zambar kuɗaɗe: Nijeriya ta karɓi milyan £4.2 na kuɗaɗen da Ibori ya wawushe – Malami

Zambar kuɗaɗe: Nijeriya ta karɓi milyan £4.2 na kuɗaɗen da Ibori ya wawushe – Malami

Daga BASHIR ISAH Babban Lauyan Nijeriya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya tabbatar cewa Gwamnatin Tarayya ta karɓi maƙudan kuɗaɗe Fan milyan £4,214,017.66 na kuɗaɗen sata da aka danganta su da iyalan tsohon Gwamnan Jihar Delta, James Ibori. Mai taimaka wa ministan kan sha'anin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Umar Gwandu, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja a ranar Talata. Bayanan Gwandu sun nuna an rigaya an saka kuɗaɗen a kwatankwacin Naira cikin asusun Gwamnantin Tarayya tun a 10 ga Mayu, 2021. Haka nan cewa Minista Malami ya rattaba hannu a takardar yarjejeniyar karɓar kuɗaɗen…
Read More
Ƙaramar Sallah: Buhari ya nemi a yi ‘Alƙunutu’

Ƙaramar Sallah: Buhari ya nemi a yi ‘Alƙunutu’

*Ɗahiru Bauchi ya ƙalubalanci Sarkin Musulmi*Tinubu ya nemi a yi wa Buhari addu’a*Saraki ya yi nasiha Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja A jiya Alihamis ne a Nijeriya da ma yawancin ƙasashen duniya aka gudanar da bikin ƙaramar Sallah ta bana, 13 ga Mayu, 2021 na shekarar Masihiyya, wacce ta zo daidai da 1 ga Shawwal, 1442 bayan Hijira, inda Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya buƙaci ’yan Nijeriya da su gudanar da addu’o’in maganta ayyukan ’yan ta’adda da kuma masu neman mulki ko ta halin ƙaƙa. Sallar idin kuma ta zo ne a daidai lokacin da fitaccen malamin addinin Islama…
Read More
Ɓarayi sun yi yinƙurin shiga gidan Ibrahim Gambari a Abuja

Ɓarayi sun yi yinƙurin shiga gidan Ibrahim Gambari a Abuja

Daga FATUHU MUSTAPHA Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar da cewa ɓarayi sun yi yinƙurin shiga gidan Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ibrahim Gambari, da ke fadar shugaban ƙasa a Abuja da subahin Litinin da ta gabata. Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu, ya ce wannan yinƙuri ne mara kan gado da ɓarayin suka yi wanda ba su kai ga cim ma manufarsu ba. A wani mai kama da wannan, Shehu ya ce a halin da ake ciki 'yan sanda sun bazama neman wani ɓarawo ruwa a jallo wanda shi ma ya yi yinƙurin shiga gidan Maikano Abdullahi…
Read More
Gwamnati ta bada hutun kwana biyu albarkacin bikin sallah

Gwamnati ta bada hutun kwana biyu albarkacin bikin sallah

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta bayyana Laraba 12 da Alhamis 13 ga Mayu, 2021, a matsayin ranakun hutu na gama-gari domin bikin ƙaramar sallah na bana. Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, shi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a Abuja a madadin Gwamnantin Tarayya. Aregbesola ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga Musulmi 'yan Nijeriya na gida da ƙetare, da su yi amfani da wannan dama wajen yi wa Nijeriya addu'ar samun zaman lafiya mai ɗorewa da daidaiton tattalin arzikin ƙasa yayin bikin na Idul Fitr. Ministan ya ce babu yadda za a…
Read More
Bikin Sallah: Buhari ya buƙaci a kiyaye dokokin korona, ya soke gaisuwar sallah

Bikin Sallah: Buhari ya buƙaci a kiyaye dokokin korona, ya soke gaisuwar sallah

Daga UMAR M. GOMBE Shugaba Muhammadu Buhari ya kira ga 'yan Nijeriya da a kula tare da lura a lokacin bikin ƙaramar sallah na bana duba da cewa har yanzu annobar korona na ci gaba da yi wa duniya barazana. Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu, ya ce a bisa dalilai na annobar korona ya sa a bana Shugaba Buhari tare da iyalansa da manyan jami’an gwamnatinsa za su gudanar da sallar Idi a cikin Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, suna masu kiyaye dokikin da aka shata din yaƙi da cutar korona. Sanarwar da Garba Shehu…
Read More
An kashe ‘yan sanda 7 a hare-haren Rivers

An kashe ‘yan sanda 7 a hare-haren Rivers

Daga UMAR M. GOMBE Rundunar 'yan sanda ta jihar Rivers ta tabbatar da mutuwar wasu jami'anta su bakwai sakamakon hare-haren da 'yan bindiga suka kai a jihar. Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, SP Nnamdi Omoni, shi ne ya tabbatar da hakan A cewar jami'in, "Maharan sun kashe jami'ansu biyu a shingen binciken abubuwan hawa a ƙauyen Choba da ke tsakanin ƙaramar hukumar Obio/Akpor da ƙaramar hukumar Emohua, sannan suka banka wa wata mota mallakar ɗaya daga cikin jami'an da lamarin ya shafa." Kazalika, ya ce 'yan bindigar sun sake kai wa ofishin 'yan sanda hari a garin Rumuji…
Read More
Allah ya yi wa ‘Maman Taraba’, Sanata Aisha Al-Hassan rasuwa

Allah ya yi wa ‘Maman Taraba’, Sanata Aisha Al-Hassan rasuwa

Daga WAKILINMU Tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Sanata Aisha Jummai Al-Hassan, wacce aka fi sani da suna Mama Taraba, ta rasu a wata asibitin ƙasar Masar, 7 ga Mayu, 2021. Wata majiya daga ahalin marigayiyar ce ta tabbatar wa Dateline Nigeria batun rasuwar. A halin rayuwarta, Jummai ta yi takarar kujerar gwamanan jihar Taraba a ƙarƙashin jam'iyyar APC a 2015. Ta riƙe muƙamin minista a gwamnatin Buhari. An haifi marigayiyar ce a Jalingo, a ranar 16 ga Satumban 1959.
Read More
Gumi da Obasanjo sun taimaka wajen kuɓutar da daliban Kaduna 27 da aka yi garkuwa da su

Gumi da Obasanjo sun taimaka wajen kuɓutar da daliban Kaduna 27 da aka yi garkuwa da su

Daga WAKILINMU Bayanai daga jihar Kaduna, sun nuna an sako ɗaliban College of Forestry Mechanisation da ke Afaka a jihar su 27 da aka yi garkuwa da su. Ɗaya daga cikin waɗanda suka karɓi ɗaliban ne ya labarta wa jaridar Daily Trust batun. Majiyar Daily Trust ta ce kwamitin sulhu na Sheikh Ahmed Gumi shi ne ya shige gaba wajen kuɓutar da ɗaliban, tare da taimakon Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo. Ɗaliban na daga cikin ɗalibai 37 da aka sace a jihar kusan watanni biyu da suka gabata. Inda bayan biyan kuɗin fansa da iyayen ɗaliban suka yi, sai 'yan…
Read More
Gwamnati ta soma nazarin rage albashin ma’aikata don rage kashe kuɗaɗe

Gwamnati ta soma nazarin rage albashin ma’aikata don rage kashe kuɗaɗe

Daga FATUHU MUSTAPHA Ga dukkan alamu, mai yiwuwa Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakin zabtare albashin ma'aikatanta a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin da take wajen ganin an rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa wajen gudanar da harkokin gwamnati. Bayanan Ministar Kuɗi, Zainab Ahmed ne suka nuna haka a Talatar da ta gabata inda ta faɗa cewa lallai, gwamnati na ƙoƙarin duba yiwuwar rage kashe kuɗaɗen da take yi wajen harkokin gudanarwa. Ta yi wannan bayani ne a wajen taron tattauna batun rashawa da tsadar gudanar da gwamnati a Nijeriya wanda Hukumar Yaƙi da Rashawa da Laifuka Masu Alaƙa da Rashawa…
Read More
Buhari ya ƙirƙiro cibiyar kula da tu’ammali da ƙananan makamai

Buhari ya ƙirƙiro cibiyar kula da tu’ammali da ƙananan makamai

Daga AISHA ASAS Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da batun ƙirƙiro Cibiyar Kula da Ƙananan Makamai ta Ƙasa (NCCSALW) wadda za ta kasance ƙarƙashin kulawar ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha'anin tsaro. NCCSALW ita ce cibiyar da za ta yi aiki a madadin Kwamitin Shugaban Ƙasa Kan Kula da Ƙananan Makamai da aka rusa. Har wa yau, za ta kasance cibiya ta bincike, yin dokoki tare da sanya ido kan harkar ƙananan makamai a Nijeriya. Tuni Shugaba Buhari ya naɗa Major General AM Dikko (Rtd) a matsayin Kodinetan da zai kula da cibiyar. Sanarwar da ta…
Read More