NBC ta dakatar da tashar Channels saboda tattaunawa da jagoran IPOB

Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), ta dakatar da gidan talabijin na Channels har da ƙarin tarar milyan N5 sabida take dokar aiki.

A wata wasiƙa da ta aike wa Manejin Daraktan tashar wadda ta sami sa hannun Muƙaddashin Babban Daraktan Hukumar, Prof. Armstrong Idachaba, NBC ta nuna ta ɗaiki wannan mataki ne ta kafa hujja da wani shirin kai-tsaye da tashar ta gabatar a ranar Lahadi, 25, Afrilu, 2021 da misalin ƙarfe bakwai na dare, inda ta kama tashar da laifin bai wa jagoran tsegerun IPOB damar faɗin maganganun da ka iya haddasa fitina ba tare wata kwaɓa ba daga tashar, wanda hakan a cewar NBC ya saɓa wa dokar aiki.

Kazalika, NBC ta zargi tashar da sakar wa baƙon nata mara inda ya zuba maganganun ƙarya game da sojojin Nijeriya duk da kotu ta bayya na su a matsayin ‘yan ta’adda.