‘Yan bindiga sun raba ƙauyuka 50 da matsugunansu a Neja – Gwamna Bello

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya ce aƙalla ƙauyuka 50 ne ‘yan bindiga suka raba da mazauninsu a tsakanin ƙananan hukumomi biyar a jihar, lamarin da a cewar gwamnan ya haifar da rikicin jinƙai a jihar.

Gwamna Bello ya bayyana haka ne a lokacin da yake buɗe taron bita na yini biyu kan inganta hanyayoyin tara kuɗaɗen shiga ga ƙananan hukumomi, a garin Minna babban birnin jihar.

Gwamnan ya ce akwai buƙatar shirya wannan taro, tare da jaddada buƙatar da ke akwai ƙananan hukumomin jihar su matse ƙaimi wajen tara wa gwamnatin kuɗaden shiga ta hanyar faɗaɗa hanyoyin tara kuɗaɗen don cim ma buƙatun gwamnati.

Ya ce kuɗaden shiga na cikin gida da ake tarawa a halin yanzu ba su wadatar gwamnati wajen cim ma buƙatunta, musamman kuma idan aka yi la’akari da ƙalubalen tsaron da jihar ke fuskanta.

Ya ci gaba da cewa, yayin da gwamnati ta dukufa wajen ganin yadda za a bunƙasa sha’anin tara kuɗaɗen shigan jihar, ya ce ya zama wajibi gwamnati ta waiwaya ta tottoshe duka ɓugagen da kuɗaɗe ke sulalewa da kuma rage kashe kuɗaɗe.

Ya ce gwammati ba za ta ɓata lokaci ba wajen kawar da ma’aikatan ƙananan hukumomin da gwamnati ba ta ƙaruwa da su.

Ta bakin gwmnan, “Yanzu haka muna da aƙalla ƙauyuka guda 50 a tsakanin ƙananan hukumomi biyar waɗanda aka raba su da matsuguninsu, ta ina za mu samu kuɗin da za mu kula da su alhali kashi 80 na kuɗaɗen gwamnati na tafiya ne wajen kula da waɗanda ba su ƙara wa gwamnati komai?

“Yanzu muna da ‘yan gudun hijira sama da 300 a garin Minna, baya ga waɗanda ake da su a sauran ƙananan hukumomin jihar.”

A ƙarshe, Gwamna Bello ya buƙaci waɗanda aka shirya taron domin su da su saka ƙwazo tare da tabbatar da an ci ma manufar taron ta yadda a ƙarshen lamari gwamnati za ta yi musu sam barka.