Tsohon gwamnan Zamfara, Yari ya faɗa komar EFCC

Daga WAKILINMU

A Talatar da ta gabata Hukumar Yaƙi da Zambar Kuɗaɗe da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa ((EFCC) ta gayyaci tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, don ya amsa mata tambayoyi kan wasu tarin zarge-zargen rashawa da aka yi masa.

Jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa a ofishin hukumar da ke Sakkwato aka tsare tsohon gwamnan na tsawon sa’o’i takwas.

Tun farko sai da EFCC ta aika wa Yari wasiƙar gayyata mai ɗauke da kwanan wata 6, Afrilu, 2021 a kan tana da buƙatar ganinsa a ofishinta na Sakkwato a ranar 8 ga Afrilu domin ya amsa mata tambayoyi.

Amma sai a Talata, 20 ga Afrilu Yarin ya amsa gayyatar da aka yi masa da misalin ƙarfe 11 na safe, in ji jaridar Premium Times.

Majiyar jaridar ta shaida cewa har zuwa ƙarfe 7 na dare na Talata, Yari na ofishin hukumar a Sakkwato.

Majiyar ta ci gaba da cewa duk da dai an bai wa Yari damar beli, sai dai ya gaza wajen cika sharuɗɗan belin da aka gindaya masa.

A cewar Premium Times, ko a Fabrairun da ya gabata, sai da ofishin EFCC na Legas ya gayyaci tsohon gwamnan inda ya zaunar da shi na tsawon lokaci tare da amsa masa tambayoyi a kan zargin yinƙurin karkatar da bilyan N300 daga asusun wani kamfani zuwa wani bankin zamani.

Duk da dai babu cikakken bayani kan harƙallar, amma Premium Times ta jiyo cewa Yari ya yi wa hukumar bayani mai tsayi kafin daga bisani ta sallame shi a wannan rana.

Kuɗaden Paris Club

Game da abin da ya shafi maido da kuɗaɗen Paris Club, nan ma Yari bai kuɓuta ba daga binciken EFCC. Domin kuwa sai da hukumar ta bincike shi dangane da sha’anin kuɗaɗen a 2017.

Bayanan da kotu ta samu daga EFCC a 2017 sun yi ƙarin haske kan yadda Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Yari ta yi biyan kuɗaɗe wanda ba a gamsu da shi ba.

Saboda an zabtare kuɗaɗen jihohi 36 fiye da abin da ya kamata a cire, wanda hakan ke da alaƙa da bashin da aka ciyo a Landan da Paris Club tsakanin 1995 da 2002.

A wani bayanin da EFCC ta miƙa wa kotu a 2017, hukumar ta nuna ta samu bayanin sirri a Janairun 2017 bisa zargin haɗa baki da goyon bayan karkatar da kuɗaɗen gwamnati har N19,439,225,871.11 daga cikin kuɗaɗen Paris Club da Gwamnatin Tarayya ta mayar don amfanin jihohin ƙasar nan su 36.

A lokacin da hukumar ke shigar da ƙara a kotu, ta nemi izinin ƙwace milyan N500 miliyan da $500,000 da ake zargin an gano a hannun Yari.

Hukumar ta ce an gano kuɗaɗen ne ɓoye a wani banki da kuma asusun kamfanin Gosh Projects Limited.

Ta ce kuɗaɗen ɓagare ne na bilyan N2.2 da aka karkatar ta hanyar zamba daga ƙungiyar NGF zuwa kamfanin BINA Consults and Integrated Services Ltd a ranar 23 ga Disamban 2016.

Biyo bayan damar da EFCC ta nema ne, ya sanya Babbar Kotu a Abuja a ranar 30 ga Yunin 2017, ta bada damar ƙwato milyan N500 da $500,000 da aka yi zambar su.

Sai dai kuma, a Nuwamba, 17, 2017, Alƙalin kotun, Nnamdi Dimgba, ya ƙi amincewa da damar da hukumar ta nema na ci gaba da shirin ƙwace kuɗaden na din-din-din tare da amince mata kan izinin farko da ta nema.

Alƙalin ya ce bai bada damar ba ne saboda an samu ɓangarori daban-daban da suka shigo suka nuna kuɗaden nasu ne.

A nata ɓangaren, ICPC ta samu umarnin ƙwace kuɗaɗe, amma wani alƙalin Babbar Kotun Tarayya, Abuja, Ijeoma Ojukwu, a ranar 26 ga watan Janairun 2021, ya bada umarnin a karɓe kuɗaɗen da ake zargi na almundahana ne da aka samu a asusun banki da ke da alaƙa da Yari.

Alƙalin ya bada umarnin haka ne bayan da hukumar ta ICPC ta shigar da takardar neman a ba ta damar haka.

An karkatar da kuɗaɗen ne ta hanyar ɓoye $56, 056.75 a bankin Polaris, sannan milyan N12.9, milyan N11.2, $301, 319.99; N217, 388.04 da kuma $311, 872.15 an ɓoye su cikin asusu daban-daban na bankin Zenith duka dai da sunan Yari da kuma kamfanoninsa.

Alƙalin ya ce Yari bai bada wani ƙwaƙƙwaran dalili ba kan abin da zai hana a bai wa ICPC damar da ta nema.