29
Apr
Daga WAKILINMU Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin mai zuwa, 3 ga Mayu, 2021, a matsayin ranar hutun ma'aikata albarkacin bikin Ranar Ma'aikata ta Duniya na bana. Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Adesoji Aregbesola, shi ne wanda ya sanar da hakan a madadin Gwamnantin Tarayya, inda ya yi amfani da wannan dama wajen taya ma'aikata a Nijeriya murnar zagayowar wannan rana. Ministan ya jinjina wa ɗaukacin ma'aikata bisa irin haƙuri da juriya da fahimtar da suke nunawa haɗa da goyon bayan da suke bai wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a ƙoƙarinta da take yi na ciyar da ƙasa gaba da…
