Gwamnatin Tarayya ta bai wa ‘Yan Nijeriya haƙuri kan ƙarancin wutar lantarki

Daga FATUHU MUSTAPHA

Gwamnatin Tarayya ta bai wa ‘yan Nijeriya haƙuri dangane da matsalar ƙarancin wutar lantarki da ake fama da ita a sassan ƙasa.

Hakan ya faru ne sakamakon akasin da aka samu a wasu cibiyoyin da ke samar wa ƙasa da lantarki, in ji Ma’aikatar Lantarki ta Ƙasa.

Mai bai wa Ministan Lantarki Shawara Kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa, Aaron Artimas, ya lissafo cibiyoyin da matsalar ta shafa da suka haɗa da cibiyar lantarki ta Sapele, ta Afam, ta Olonrunsogo, ta Omotosho, ta Ibom, ta Egbin, ta Alaoji, da kuma ta Ihovbor.

Ya ƙara da cewa an kashe cibiyar lantarki ta Jebba domin kula da na’urorin kamar yadda aka saba duk shekara, yayin da kuma cibiyar Shiroro ke fama da matsalar ruwa.

Kazalika, ya ce wasu cibiyoyin guda bakwai, wato ta Geregu da Sepele da Omotosho da Gbarain da Omuku da Paras da kuma ta Alaoji baki ɗaya suna fama da matsalar ƙarancin gas.

Artimas ya koka kan mummunan halin da cibiyoyin ke ciki wanda hakan ya yi sanadiyar raguwar wutar lantarkin da ƙasa ke samu.

A wasu jerin saƙonnin da ya wallafa a shafinsa na twita, Ministan Lantarki, Sale Mamman, ya nuna rashin jin daɗin game da halin da fannin lantarkin ƙasar nan ya tsinci kansa a ciki. Tare da bai wa ‘yan Nijeriyar da matsalar wutar ta shafa haƙuri.

Sannan ya bai wa ‘yan ƙasa tabbacin cewa ma’aikatarsa tare da haɗin gwiwar hukumomin da suka dace na nan na ci gaba da aiki babu kama hannun yaro domin mangace matsalar ƙarancin gas da sauransu.