Nijar: Yadda gobara ta ci ƙananan yara 20 a makaranta

Daga BASHIR ISAH

Ƙananan yara ‘yan makaranta kimanin su 20 aka ruwaito sun halaka a ƙasar Nijar sakamakon gobarar da ta auku a wata makaranta.

Wannan mummunan al’amari ya faru ne a Talatar da ta gabata a gefen Niamey, babban birnin ƙasar, inda iyaye da malamai haɗa da sauran al’ummar yankin suka kasance cikin alhini mara misaltuwa.

Gobarar ta ci yaran ne a cikin azuzuwan da aka gina da katakai, kamar yadda shaidu suka bayyana.

Daraktar makarantar, Habiba Gaya, cikin kuka da hawaye ta faɗa wa jaridar AFP cewa haka yaran suka ƙone a cikin gobarar. Ta ce wasu daga cikin yaran sun kuɓuta ma ibtila’in yayin da wasusunsu suka cim ma ajalinsu.

Ta ce galibin yaran da suka rasu ɗin ‘yan shekara biyar ne zuwa ƙasa. Tare da cewa ƙarancin shekarun yaran ya sa suka kasa ficewa.

Ya zuwa haɗa wannan labari, ba a kai ga gano musabbabin aukuwar gobarar ba.

Kwamandan Hukumar Kashe Gobara na Nijar, Sidi Mohamed, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce yara kimanin su 20 ibtila’in ya rutsa da su.

Kawo yanzu, al’ummar yankin da lamarin ya faru na ci gaba da nuna alhininsu, sannan jami’an tsaro sun killace wurin don zurfafa bincike.