Imo: Yadda IPOB ta kai hari kan gidan yari da hedikwatar ‘yan sanda

Daga WAKILINMU

‘Yan Ƙungiyar Jama’ar Biafra (IPOB) sun kai mummunan hari kan ofishin ‘yan sanda da kuma gidan yari a Owerri babban birnin jihar Imo, inda suka yi sanadiyar tserewar fursunoni da dama

‘Yan ƙungiyar wanda da ma ana zarginsu da kashe jami’an tsaro a shiyyar Kudu-maso-gabas, sun kai harin ne ta hanyar banka wuta a gine-gine da motoci da sauran kayayyaki.

Majiyar Manhaja ta ce maharan sun yi amfani da abubuwa masu fashewa da kuma bindigogi wajen kai harin. Ta ci gaba da cewa an ji fashewa mai ƙara da kuma harbe-harben bindiga a yankin.

Yayin harin, wasu daga cikin fursunonin sun yi amfani da wannan dama wajen arcewa, yayin da wasunsu kuwa suka zaɓi su tsaya.

Bayanai sun nuna lamarin ya auku ne da misalin karfe ɗaya na daren Litinin inda wasu ‘yan ƙungiyar IPOB/ESN suka far wa gidan yarin Owerri ɗauke da makamai.

A harin da suka kai wa Babban Ofishin ‘Yan Sanda na Owerri, an ce maharan sun yi harbe-harbe da bindigogi ƙirar AK47 da sauraran abuwabuwa masu fashewa inda a nan suka yi dalilin kuɓucewar wasu da ake tsare da su a hannun SCID, tare da ƙona ofisoshi da motoci da dama a harabar ofishin.

Mai magana da yawun gidan yarin da harin ya shafa, ya ce za su fitar da bayani a hukumance da zarar sun kammala haɗa bayanansu kan ɓarnar da aka tafka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *