Kwara: An samu ɓarkewar rikicin kabilanci a ƙaramar hukumar Edu

Daga AISHA ASAS

Bayanan da Manhaja ta samu daga jihar Kwara sun nuna an samu ɓarkewar rikicin ƙabilanci tsakanin al’ummar Tsaragi da maƙwabtansu na Kange a yankin ƙaramar hukumar Edu, lamarin da ya yi sanadiyar mutane da dama sun ji rauni.

Duk da dai ba aka ga fayyace dalilin aukuwar rikicin ba ya zuwa haɗa wannan labari, amma binciken Manhaja ya gano babu ko mutum guda da ya rasa ransa sakamakon rikicin wanda ya faru a ranar Alhamis.

Sai dai wata shaida ta tabbatar cewa an samu mutane da dama daga ɓangarorin biyu waɗanda suka jikkata yayin hatsaniyar.

Jami’i mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da aukuwar rikicin.

Ajayi ya ce tuni jami’ansu suka shiga suka lafar da ƙurar da aka tayar a inda a ƙarshe aka tabbatar da lumana a yankunan.

Haka ita ma gwamnatin jihar Kwara, ta ce ta ɗauki matakin samar da wanzajjen zaman lafiya a ƙauyukan Tsaragi da Kange.