Kaduna: NLC ta nuna rashin amincewarta kan matakin sallamar ma’aikata

Daga FATUHU MUSTAPHA

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) reshen jihar Kaduna ta ƙi amincewa da shirin korar ma’aikata da maida wasunsu ma’aikatan wucin-gadi a jihar.

Ƙungiyar na ra’ayin cewa ɗaukar wanna mataki zai ƙara tsananta matsalar tsaro da kuma ƙalubalen tattalin arzikin da ake fama da su a jihar.

Da suke yi wa manema labarai bayani kan batun jim kaɗan bayan kammala taron shugabannin ƙungiyar na jiha, Shugaban NLC na Kaduna, Comrade Ayuba Magaji Suleiman da Sakatariyarsa Comrade Christiana John Bawa, baki ɗaya sun yi kira ga gwamnatin Kaduna da ta janye wannan shiri nata sannan ta lalubo hanyar da ta fi dacewa wajen gudanar da harkokinta ba tare da muzgunawa talakawanta ba.

A cewar NLC, “Ranar Talata 6 ga Afrilu, 2021, an miƙa wa dubban ma’aikatan ƙananan hukumomin jihar takardar sallama daga aiki. Kuma an yi wannan ne ba tare da wani tsari na biyan giraduti ga waɗanda lamarin ya shafa ba wanda hakan kuwa ya saɓa ma sashe na 210 na Kundin Tsarin Mulkin Kasa na 1999 wanda ya tabbatar da haƙƙin biyan fansho ga ma’aikacin gwamnati.

“A baya-bayan nan Gwamnantin Jihar Kaduna ba tare da la’akari da matakan da suka dace ba ta sake shirya wata takarda ta aika wa Shugaban Ma’aikata na Jihar a matsayin wani mataki na shirin sake dakatar da wasu ma’aikatanta daga aiki.”

Bisa wannan dalili ne NLC ta ce tana buƙatar gwamnati ta lura da abubuwan da suka dace kafin ɗaukar irin wannan mataki.

Ta ce ya zama wajibi gwanatin ta yi la’akari da abin da ka je ya komo dangane da koran ma’aikata da yawa a lokaci guda kamar haka, musamman ma abin da ya shafi tsaron jihar da kuma sha’anin tattalin arziki.

Tana mai cewa matakin dakatar da ma’aikatan tamkar ƙara wa al’ummar jihar raɗaɗin matsin rayuwa ne wanda da ma suke fama da shi.

“Yayin da za mu kasance kanmu a haɗe da kuma bibiyar gwamnati da masu faɗa a ji na jihar ta hanyar da ta dace domin samun maslaha, haka nan muna fatan fitattun ‘yan jihar da sauran jama’a za su shigo su mara wa NLC baya don haƙa ta cim ma ruwa”, in ji NLC.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*