Imo: ‘Yan bindiga sun sake kai hari a ofishin ‘yan sanda

Harin da aka kai wa gidan yarin Owerri

Daga WAKILINMU

‘Yan bindiga a jihar Imo sun kai hari a babban ofishin ‘yan sanda na Mbieri cikin yankin ƙaramar hukumar a jihar Imo.

Harin wanda ya auku ranar Laraba da tsakar dare, ha yi sanadiyar tserewar wasu da ake tsare da su a ofishin.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na ‘Yan Sandan Jihar, Orlando Ikeokwu, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Inda ya ce ɗaya daga cikin jami’ansu ya ɓata yayin da wasu jamiai biyu sun ji rauni sakamakon farmakin.

Haka nan, Ikeokwu ya tabbatar cewa maharan sun kuɓutar da wasu da ake tsare da su a ofishin ‘yan sandan.

Wannan na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 48 bayan harin da ‘yan bindigar suka kai a gidan yari da kuma ofishin ‘yan sanda a Owerri

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *