Haramtattun makamai sama da milyan 6 ake ta’ammali da su a Nijeriya – Abdulsalam

Andulsalam

Daga UMAR M. GOMBE

Tsohon Shugaban Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Zaman Lafiyar Ƙasa, General Abdulsalami Abubakar (mai murabus) ya yi jan hankali a kan yadda ta’ammali da bindigogi ke daɗa ƙaruwa a Nijeriya.

Yana mai cewa a halin da ake ciki a ƙiyasce bindigogi milyan shida ne ake ta’ammali da su a faɗin ƙasa ba a bisa ƙa’ida ba.

Abdulsalam ya ce ƙaruwar ta’ammali da makamai ya tsananta matsalar tsaro a ƙasa wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutum sama da 80,000 tare da raba mutane kusan milyan uku da gidajensu.

Abubakar ya yi waɗannan bayanai ne a wajen taron tattaunawar da kwamitinsa ya gudanar tare da wasu masu ruwa da tsaki a Abuja a ranar Laraba.

Tsohon Shugaban Ƙasar ya lissafo ƙalubalan da ke fuskantar Nijeriya da suka haɗa da ta’addancin Boko Haram da fashin daji da sace-sacen mutane da ƙaruwar talauci da kira kan sake fasalin ƙasa da barazanar yunwa sakamakon rashin tsaro da manoma ke fuskanta da dai sauransu.

A cewar Abdulsalam, “Abin damuwa ne matuƙa ganin yadda ake samun ƙaruwar ta’ammali da makamai. An ƙiyasta cewa akwai makamai sama da milyan shida da ake ta’ammali da su a ƙasar nan, wanda hakan ya ƙara zafafa matsalar tsaron da ta yi dalilin mutuwar mutane sama da 80,000 sannan kusan mutum milyan uku sun rasa matsugunansu.”

Game da bayan da kwamitinsa ya tattara kan sha’anin tsaron ƙasa, Andulsalam ya ce akwai ƙarancin jami’an tsaro, rashin ƙarfafabwa jami’an yadda ya kamata da kuma rashin isasshen kuɗi. Yana mai cewa jami’an tsaron za su yi fiye da yadda ake zato muddin aka wadata su da ingantattun kayayyakin aiki da kuma kuɗi.

Ta bakin Abdulsalam, “Mun yarda cewa wajibi ne Nijeriya ta lalubo hanyar da za ta bi wajen magance waɗannan matsaloli. Fatanmu shi ne baya ga bayyana halin da tsaron ƙasa ke ciki, za kuma mu haɗu mu bada shawarwarin da za su taimaka wajen dasa ƙwarin gwiwa a zukatan ‘yan ƙasa da kuma tabbatar da ƙasa ta ci gaba da zama dunƙulalliya.”

Mahalarta taron sun haɗa da, Sultan na Sakkwato, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III; John Cardinal Onaiyekan; Gwamnan Ekiti kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya, Kayode Fayemi; Gwamnan Plateau kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Simon Lalong, Shugaban jaridun Manhaja da Blueprint, Mohammed Idris Malagi, Shugaban jaridar Daily Trust, Kabiru Yusuf, shugabannin addinai, sojoji, ‘yansanda da takwarorinsu, da sauransu.

Abdulsalam Abubakar ya ce Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yana sane da taron kuma ya nuna goyon bayansa. Tare da cewa an shirya taron ne da zummar gano matsalolin da suka dabaibaye ƙasa da kuma matakan da suka dace a yi amfani da su wajen magance su.

Yayin da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron, Alhaji Aliko Dangote wanda mamba ne a kwamitin, ya yi magana a kan irin rawar da ‘yan jarida ke takawa wanda a cewarsa hakan na haifar da yi wa ƙasa kallo da ido mara kyau.

Daga nan ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su zama masu lura da bayanan da suke yaɗawa don kauce wa sanyaya wa ‘yan kasuwa gwiwa shigowa ƙasa don zuba jari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *