Gumi da Obasanjo sun yi ganawar sirri

Daga FATUHU MUSTAPHA

Fitaccen malamin Islman nan na Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi wata ganawar sirri tare da Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta babban birnin jihar Ogun, a Lahadin da ta gabata.

Wata majiya ta kusa da taron, ta ce Gumi ya zaɓi ganawa da Chief Obasanjo ne kasancewarsa na mai faɗa a ji a cikin ƙasa kuma wanda al’umma ke girmamawa.

Malamin ya labarta wa Obasanjo ziyarar da ya kai wa Fulani masu fashi a Arewacin ƙasa da zummar gwamnati ta yi wa yanayin kyakkyawar fahimta da kuma yin aiki da shawarwarin da bayar a matsayin hanyar da za a kawo ƙarshen matsalolin tsaron da suka addabi ƙasa a wannan lokaci.

Takardar bayanin da ta sami sa hannun Obasanjo da Gumi a ƙarshen ganawar tasu, ta nuna su biyun sun yi ittifaƙin cewa matsalolin sace-sacen mutane, fashin daji, ta’addanci da sauran manyan laifuka da ake aikatawa su ne suka haifar da rashin tsaro a ƙasa, kuma abu ne da ya shafi ƙasa baki ɗaya.

Sun nuna cewa na daga cikin dalilan da suka haifar da taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya rashin karatu da rashin daidaiton tattalin arzikin ƙasa, sai kuma amfani da addini ta hanyar da ba ta dace ba haɗa da ƙabilanci da kuma sha’anin siyasa.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*