Kada ‘yan Nijeriya su yanke tsammanin samun daidaiton Nijeriya – Osinbajo

Osinbajo

Daga UMAR M. GOMBE

Mataimakin Shugaban Ƙasa Professor Yemi Osinbajo, ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su zamo masu kyautata zato tare da fatan harkoki za su daidaita a ƙasa.

Osinbajo ya faɗi haka ne yayin wata ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala ibadar Easter a mujami’ar Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a Lahadin da ta gabata.

A cikin sanarwar da hadiminsa kan sha’anin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Laolu Akande ya fitar, Osinbajo ya ce yana da yaƙinin rahma da albarkar Ubangiji za su lulluɓe Nijeriya.

Sanarwar mai taken ‘Saƙon bikin Easter na Osinbajo zuwa ga ‘yan Nijeriya: Komai na ƙasarmu za su daidaita’, ta buƙaci kada ‘yan Nijeriya su yanke tsammani kan cewa gaba zai fi baya kyau.

Osinbajo ya yi wa ‘yan Nijeriya fatan a yi bikin Easter lafiya tare ɗabbaƙa ɗabi’ar son juna da taimakekeniya.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*