Matawalle: APC ta yi babban kamu a Zamfara

Daga AISHA ASAS

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya kammala shirin sauya sheƙa daga jam’iyyarsu ta PDP zuwa APC inda ake sa ran shugaban riƙo na APC, Mai Mala Buni ya gabatar da shi ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna mai yiwuwa a kammala komai idan tawagar Gwamnatin Tarayya ta ziyarci Zamfara a ranar Talata domin jajanta wa gwamnan game da ibtila’in gobarar kasuwa da ya auku kwannan nan a jihar.

Tun ba yau ba, wasu gwamnoni masu ci tare da tsohon gwamnan Zamfara, Ahmed Sani Yerima, na daga cikin gaggan ‘yan siyasar da suka yi zawarcin Matawalle ya koma APC domin karya lagon tsohon gwamna Abdulaziz Yari a jam’iyyar.

Yari wanda a can baya ya kasance ɗan gidan Yarima a siyasance, ya yi kaurin wuyan da sai abin da yake so za a zartar a APCn Zamfara.

Yarima ya soma bayyana aniyar Matawalle ta komawa APC ne tun a wata hira da aka yi da shi a Farairun da ya gabata.

Sai dai wata majiya mai tushe ta rawaito Yari ya sha alwashin ba zai ci gaba da zama a APC ba daga ranar da Matawalle ya sauya sheƙa ya shigo cikin ta.

Ana ganin matakin barin PDP da Matawalle ya ɗauaka ba ya rasa nasaba da faɗar da gwamnan ya yi a baya cewa PDP ba ta bai wa gwamnoninta haɗin kan da ya kamata.

A Nuwamban da ya gabata, Gwamna Matawalle ya yi ƙorafi a kan yadda gwamnonin PDP suka juya masa baya a daidai lokacin da yake da buƙatar su. Tare da bada misalin yadda gwamnonin PDP na Kudu-maso-kudu suka yi ta watangaririya da shi a jaridu.

Har wa yau, ya ce gwamnonin ne suka haifar da ruɗani kan batun zinari a Zamfara ta hanyar kitsa ƙarya da yaɗa bayanan boge.

“Abin mamaki, sai gwamnatin APC ce ta tattara sahihan bayanai dangane da batun zinari a Zamfara ta kuma fito ta kare ni daga wannan dambarwar.

“A matsayin ‘yan’uwa a PDP, na yi zaton gwamnonin su soma jin tabakina domin sanin yadda al’amarin yake kafin su shiga jaridu suna yaɗa munanan maganganu”, in ji Matawalle.

Daga nan, Matawalle ya nuna godiyarsa ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari dangane da irin goyon bayan da yake ba shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *