‘Yan bindiga sun yi kaca-kaca da ofishin ‘yan sanda a Imo

Spread the love

Bayanan da Manjaha ta samu ba da jimawa ba daga jihar Imo, sun nuna wasu ‘yan bindiga da ba a kai ga sanin ko su wane ne ba a jihar, sun kai wa sabon hedikwatar ‘yan sanda na ‘Zone 13’ da ke Ukpo hari inda suka banka wa ofishin wuta suka yi kaca-kaca da shi.

Binciken Manhaja ya gano cewa ‘yan sanda biyu sun rasu sakamakon harin, yayin da motoci da dama sun ƙone.


Ƙazamin harin wanda aka kai a wannan Litinin, ya zuwa haɗa wannan labari hukumomi ba su ce komai a kai ba.

Ko a ‘yan makonnin da suka gabata, sai da ‘yan bindigar suka kai hari a babban ofishin ‘yan sanda na Imo da kuma gidan yarin Owerri inda gomman fursunoni suka tsere.

By Editor