Zanga-zanga: An hana lauyoyi shiga Majalisar Tarayya

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Jami’an tsaro a Abuja, sun hana tawagar lauyoyi da suka yi zanga-zanga shiga Majalisar Tarayya.

A wannan Litinin mambobin Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA) suka gudanar da zanga-zangar lumana zuwa Majalisar inda suka tarar da jami’an tsaro girke a ƙofar shiga majalisar.

Manhaja ta gano cewa lauyoyin sun yin zanga-zangar ne domin nuna goyon baya da haɗin kai ga ma’aikatan fannin shari’a dangane da ‘yancin gashin kan da suke nema na sarrafa kuɗaden gudanarwa.

Tun farko sai da lauyoyin suka yi dafifi a ƙofar shiga Kotun Ɗaukaka Ƙara kafin daga bisani suka ɗunguma zuwa Majalisar Tarayya inda suka bayyana buƙatarsu.

Amma ko da jami’an tsaro suka tsinkaye su, sai suka garƙame ƙofar shiga majalisar kafin ƙarasowarsu.

A Juma’ar da ta gabata Shugaban NBA na Ƙasa ya bai wa shugabannin rassan ƙungiyar na jihohi 36 kan su ziyarci fadar gwamnoni a jihohinsu dangane da zargin da aka yi cewa gwamnonin na take-taken ƙin yarda da ‘yancin gashin kai na fannin shari’a.

Sanarwar da ƙungiyar ta fitar ta hannun Olumide Akpata, ta umarci duka shugabannin rassanta na jihohi da su jagoranci kai ziyara mai kama da zanga-zangar lumana ya zuwa gidan gwamnati na kowace jiha a wannan Litinin da kuma kowace Litinin a gaba har sai haƙarsu ta cim ma ruwa.

Tun 6 ga Afrilu, 2021 Ƙungiyar Ma’aikatan Fannin Sharia ta Ƙasa (JUSUN) ta yi silar zama kotuna a rufe saboda rashin aiwatar mata da ‘yancin gashin kai kan sha’anin kuɗi kasancewar fannin a matsayin matakin gwamnati na uku.

JUSUN ta tsunduma yajin aikin gama gari ne tun ranar 19, 2021.

By Editor