Yanzu-Yanzu: Kotu ta yanke wa ɗan China hukuncin kisa kan kisan Ummita a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Babbar Kotun Jihar Kano, ta yanke wa ɗan Chinan nan, Frank Geng Quarong hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji ne ya yanke masa hukuncin, bayan tabbatar da hujjojin da masu gabatar da ƙara suka yi a gaban kotun.

Idan za a iya tunawa Manhaja ta rawaito tun a ranar 16 ga watan Satumba 2022, Frank Geng, ya hallaka Ummita a unguwar Janbulo da ke jihar Kano.