Rundunar Soji za ta saki mutum 200 da ke tsare bayan wanke su daga zargin alaƙa da Boko Haram

Daga BASHIR ISAH

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ta shirya sakin sama da mutum 200 da taje tsare da bayan wanke su da aka yi faga zargin samun alaƙa Boko Haram.

A tsare waɗanda lamarin ya shafa ne a mabambantan hare-hare da sojoji suka kai a wurare daban-daban game da yaƙi da mayaƙan Boko Haram.

MANHAJA ta kalato cewar, za a miƙa mutanen ne ga Gwamnatin Jihar Borno domin yin abin da ya dace kafin a sake sada su da ‘yan uwansu.

A wannan Talatar ake sa ran lamarin zai wakana a Barikin Sojoji da Giwa a Maiduguri, babban birnin jihar.

Majiyarmu ta ce, “Aƙalla mutum 200 ne aka wanke su daga zargin Boko Haram, kima za a miƙa su ga Gwamnatin Borno domin inganta rayuwarsu kafin miƙa su ga ‘yan uwansu.”