Tsaro: Lawal ya buƙaci a tura ƙarin dakaru zuwa Zamfara

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya yi kira da a ƙara yawan sojojin da ke aiki a jiharsa domin ci gaba da yaƙi da matsalolin tsaro a jihar.

Lawal ya yi wannan kira ne a ranar Litinin yayin da da ya ziyarci Babban Hafsan Tsaro, Christopher Gwabin Musa, a ofishinsa da ke Abuja.

Mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya faɗa cikin sanarwar da ya fitar cewa, Lawal ya ziyarci Babban Hafsan ne domin tattauna batutuwan da suka shafi tsaro a Jihar Zamfara.

Ya ce, yayin ganawar tasu, Gwamna Lawal ya nuna damuwa kan yadda ake samun ƙaruwar hare-haren ta’addanci a wasu sassan Zamfara.

Daga nan ya miƙa buƙatarsa ga Shugaban Tsaron kan a tura ƙarin dakaru da makaman da suka dace zuwa jihar.

Sanarwar ta rawaito Lawal na cewa, “Jiya an kai hari a yankin ƙaramar hukumar Tsafe wanda ya haifar da asarar rayuka ciki har da jami’in Dakarun Tsaron Al’umma (CPG). Kuma an ƙona motocin sojoji da na CPG.

“Muna fuskantar ƙarancin sojoji a Zamfara sakamakon an tura wasunsu zuwa shiyyar Arewa maso-Gabas.

“Manoma ba sa iya tafiya gona, sannan rayuka da yawa sun salwanta sakmakon hare-haren.

“Don haka nake amfani da wannan dama wajen kira da a tura ƙarin dakaru zuwa Zamfara. Ɗaukar wannan matakin na matuƙar muhimmanci domin daƙile barazar tsaro da kuma tabbatar da luma a yankin,” in ji Lawal.

A nasa jawabin, Janaral Christopher Gwabin Musa, ya yaba wa ƙoƙarin da Gwamna Lawal ke yi wajen yaƙi da ta’addanci a jihar Zamfara.

Ya ce, “Muna shirin sake ɗamara domin yaƙi da matsalolin tsaro ta hanyar amfani da dabarun da muka yi amfani da su wajen murƙushe ‘yan ta’adda a Maiduguri.”