Babban Labari

Farfesa Yakubu ya yi bankwana da shugabancin INEC

Farfesa Yakubu ya yi bankwana da shugabancin INEC

*Shine mafi daɗewa a jagorancin hukumar *Tinubu ya karrama Yakubu da lambar CON *Majalisar ƙasa ta amince da Amupitan matsayin sabon shugaba Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya sauka daga muƙaminsa tare da miƙa ragamar jagorancin hukumar ga May Agbamuche-Mbu, wacce za ta riƙe muƙamin a matsayin na riƙo kafin naɗa sabon shugaba. Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin ganawa da kwamishinonin hukumar a hedikwatarta da ke Abuja bayan ya shafe shekarru 10 a kan muƙamin, inda ya kasance shugaban hukumarr zaɓe a Nijeriya…
Read More
Shekaru 65 da ‘yanci: Daga yanzu wahala ta ƙare – Tinubu

Shekaru 65 da ‘yanci: Daga yanzu wahala ta ƙare – Tinubu

*Cikin shekaru biyu mun samu gagarumin cigaba, inji Shugaban ƙasa *Yunwa na kashe ’yan Nijeriya, amma ko a jikin Tinubu – Atiku *Kada ku yanke ƙauna da cigaban ƙasa – Jonathan ga 'yan Nijeriya *Akwai buƙatar kishin ƙasa da haɗin kan al’umma, inji Sarkin Kasuwar Beirut Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce, gwamnatinsa ta samu gagarumin cigaba a fannoni daban-daban cikin shekaru biyu da suka gabata, duk da ƙalubalen tattalin arziki da tsaro da ƙasar ta fuskanta. A jawabin da ya gabatar yayin bikin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, Shugaba…
Read More
Shugaban FRSC: Ba za mu iya aiki babu bindiga ba

Shugaban FRSC: Ba za mu iya aiki babu bindiga ba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa (FRSC), Corps Marshal Shehu Mohammed, ya ce, bai wa jami’an kiyaye haɗura makamai na iya zama hanya ɗaya tilo da za a iya aiwatar da dokokin hanya yadda ya kamata a kan manyan titunan Nijeriya da ke ƙara taɓarɓarewa. Yayin da ya ke magana a gidan Talabijin na Arise News a jiya Alhamis, inda Blueprint Manhaja ta sa a kai, shugaban hukumar ta FRSC ya zayyano ƙalubalen da jami’ansa ke fuskanta a lokacin da suke fuskantar manyan motoci da tankokin mai da tireloli masu yawa. "Yaya za ka…
Read More
Yadda taƙaddamar Ɗangote da NUPENG ta ke ƙazancewa

Yadda taƙaddamar Ɗangote da NUPENG ta ke ƙazancewa

*Rikicin zai iya tsorata masu son zuba jari a Nijeriya, a cewar masana *Kotu ta yi allawadai da umarnin rufe Matatar ɗangote Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rikici ya sake ɓarkewa tsakanin rukunin kamfanonin ɗangote da ƙungiyar Ma’aikatan Mai da Iskar Gas ta Nijeriya, NUPENG a taƙaice. Wannan sabon rikici ya ɓarke ne kwanaki bayan hukumar DSS ta jagoranci sulhu a tsakanin ɓangarorin biyu, kan ƙungiyanci a matatar Dangote. Rikicin ya kunno kai ne bayan an umarci direbobin motocin mai na MRS da su cire tambarin ƙungiyar NUPENG da aka manna a motocinsu. Wannan mataki ya fusata shugabannin ƙungiyar NUPENG, inda…
Read More
Muhimman abubuwa kan harajin kashi biyar na fetur

Muhimman abubuwa kan harajin kashi biyar na fetur

*Zai samar da titina masu aminci – Shugaban kwamitin Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ’yan makonnin nan, gwamnati ta sake jawo ce-ce-ku-ce a Nijeriya bayan da aka sanar da batun ƙarin haraji na ƙashi 5 a kan man fetur. Wannan ya sa mutane da dama suke tambayar: Shin sabon haraji ne? Yaushe za a fara aiwatar da shi? Kuma mene ne manufar gwamnati? Shugaban kwamitin shugaban ƙasa da ke tsare-tsare da yi wa tsarin haraji garambawul, Taiwo Oyedele, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na ɗ cewa ba sabon haraji ba ne gwamnatin…
Read More
Zamfara: Yadda na san zirga-zirgar ’yan bindiga – Dauda

Zamfara: Yadda na san zirga-zirgar ’yan bindiga – Dauda

Daga MAHDI MUSA MUHAMMMAD Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya ce, ya san komai kan zirga-zirgar jagororin ’yan bindiga a jiharsa, yana mai cewa, za su zama tarihi idan har yana da iko kan hukumomin tsaro. Gwamna Dauda, a cikin wani faifan bidiyo da ya yaɗu, ya bayyana cewa, ya san ainihin wuraren da ’yan bindigar suke ɓuya. Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa, yana sane da ainihin wuraren da manyan shugabannin ’yan bindigan da ke addabar jihar suke. Gwamna Dauda Lawal ya kuma koka kan yadda yaƙi da 'yan bindiga ya ke kwan-gaba-kwan-baya a jihar. Ya bayyana cewa,…
Read More
Sanusi Sami ya zama sabon Sarkin Zuru 

Sanusi Sami ya zama sabon Sarkin Zuru 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi ya amince da naɗin Alhaji Sanusi Mika’ilu Sami a matsayin sabon Sarkin Zuru. Naɗin nasa ya biyo bayan rasuwar tsohon Sarki Muhammad Sani Sami Gomo II, wanda ya rasu a ranar 16 ga Agusta, 2025, a wani asibitin Landon. Yayin da ya ke gabatar da takardar naɗin ga sabon sarkin jiya Alhamis a garin Zuru, Kwamishinan ƙananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Kebbi, Alhaji Garba Dutsin-Mari, ya ce, naɗin ya biyo bayan shawarar kwamitin zaɓen. Dutsin-Mari ya ce daga cikin ‘yan takara uku da suka nemi wannan muƙami…
Read More
Ambaliya: Yadda jihohin Arewa suka shiga uku

Ambaliya: Yadda jihohin Arewa suka shiga uku

*Ta halakar da mutum 165 *Ta shafi mutane 119,0000 *Ta lalata gonaki 8,200 *Mutum 43,936 sun rasa matsuguni Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD a Kaduna da JAMIL GULMA a Birnin Kebbi  Nijeriya, musamman a arewacin ƙasar, na fama da ɗaya daga cikin manyan bala'o'i a duniya ta ambaliyar a cikin 'yan shekarun nan, inda aka tabbatar da mutuwar mutane aƙalla 165, yayin da ta shafi wasu sama da 119,000 cikin jihohi 19 na ƙasar ya zuwa ranar 16 ga Agusta, 2025. Rrahoton Hukumar Gidan Talabijin ta Nijeriya (NTA) ce ta bayyana wannan ƙididdigar ta hanyar asusunta na ɗ, wanda ta ba…
Read More
Babu sasanci tsakaninmu da Turji, inji Hedikwatar Tsaro

Babu sasanci tsakaninmu da Turji, inji Hedikwatar Tsaro

*Ta ƙaryata malamin da ya ce an yi sulhu *Har yanzu muna neman Turji ruwa a jallo, cewar jami’an tsaro *Yadda ƙananan hukumomin Katsina ke yin sulhu da 'yan bindiga *Yadda yaran Turji suka sake sake aikata ta’addanci a Sakkwato Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD da BELLO A. BABAJI a Abuja da ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hedikwatar Tsaron Nijeirya ta musanta rahotannin da ke cewa ƙasurgumin ɗan bindigar nan, Bello Turji, ya miƙa wuya a ƙarƙashin wata yarjejeniyar zaman lafiya da wasu malaman addinin Musulunci suka yi da shi a Jihar Zamfara, lamarin da ke nunu da cewa, ba lallai nde…
Read More
Tinubu ya yi dirar mikiya kan almundahanar kurkuku

Tinubu ya yi dirar mikiya kan almundahanar kurkuku

*An kori jami'ai 15 tare da hukunta 59 Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kori jami'ai 15 na Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta ƙasa (NCoS) tare da rage matsayin wasu 59 saboda aikata laifuka da rashin ɗa’a a wuraren aiki daban-daban. Wannan na cikin sanarwar da Hukumar CDCFIB, Mai Kula da Harkokin Hukumomin Sibil Defens, Gudajen Gyaran Hali, Kashe Gobara da Shige da Fice ta fitar ne. Sanarwar ta ce, an ɗauki wannan matakin ne bayan nazari kan hukuncin ladabtarwa da suka shafi jami’an hukumar daga sassa daban-daban na ƙasar.…
Read More