01
Aug
Daga JAMILU GULMA, a Kebbi Al'ummar yankin garuruwan Libata da Lokon-Uba da Kabiriba da sauran ƙananan ƙauyuka da ke ƙaramar Hukumar Mulki ta Ngaski da ke Jihar Kebbi sun koka bisa ga yadda kamfunnan haƙar ma'adanai a yankin ke cin karen su ba babbaka yayin da aka mayar da al'ummomin yankin ’yan kallo ba tare da wani ihsani ba ko samar da abubuwan more rayuwa ba. Malam Sani Aliyu daya ɗaga cikin matasan yankin kuma mai sana'ar kabu-kabu (acaba)ya bayyana wa wakilinmu cewa, waɗannan mutanen sun daɗe suna cin karen su ba babbaka a yankin wajen haƙar ma'adanai da su…
