Babban Labari

2027: Gwamnoni da ’yan majalisa sun yi wa Tinubu mubayi’a

2027: Gwamnoni da ’yan majalisa sun yi wa Tinubu mubayi’a

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gabanin fara yaƙin neman zaɓen 2027, ƙungiyar Gwamnonin jam’iyyar APC ta amince da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027. Wannan ya zo ne a daidai lokacin da su ma ’yan majalisar dokoki na jam’iyyar APC ɗin suka amince da takarar ta Shugaban ƙasa. ƙungiyar gwamnonin ta amince da Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takara ɗaya tilo na jam’iyyar domin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027. Gwamnan jihar Imo kuma shugaban ƙungiyar, Hope Uzodimma, ne ya sanar da wannan matsaya a taron ƙoli na jam’iyyar APC da aka gudanar a Abuja.…
Read More
Ana shirin ɗaure waɗanda suka ƙi yin zaɓe

Ana shirin ɗaure waɗanda suka ƙi yin zaɓe

*Ƙudirin ya tsallake karatu na biyu Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙudirin da zai yi wa dokar zaɓe ta 2022 kwaskwarima, domin sanya wa ‘yan Nijeriyar da suka kai shekarun kaɗa ƙuri’a dole ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai. Shugaban majalisar, Tajjudeen Abbas, da Daniel Ago ne suka ɗauki nauyin wannan ƙudurin dokar. Da yake jagorantar muhawarar yayin zaman majalisar a ranar Alhamis, Ago ya ce ƙudirin na da nufin ƙarfafa gwiwar 'yan ƙasa a cikin tsarin zaɓe, tare da lura da cewa za a magance rashin jin daɗin masu kaɗa ƙuri'a a lokacin zaɓuka idan ƙudirin…
Read More
Rikicin cikin gida: Yadda jam’iyyun adawa suka rasa kataɓus

Rikicin cikin gida: Yadda jam’iyyun adawa suka rasa kataɓus

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Batun sauyin sheƙar ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyya mai mulki ya haifar da muhawara kan gaskiyar da ƙimar jam’iyyun. Kusan shekaru biyu kenan tun bayan zaɓen 2023, jam’iyyar APC ta kasance ko dai ta kutsa ko ta mamaye jam’iyyun adawa. Masu rajin kare haƙƙin ɗan adam da masu nazarin al’amura sun ce, rashin wata jam’iyyar adawa mai ƙarfi ya haifar da rauni ga dimukraɗiyyar Nijeriya, domin bibiyar ɓangaren zartarwa ya jawo ƙarancin bayanai game da ayyukan gwamnati. A kwanakin baya ne gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ɗan jam’iyyar adawa ta PD,…
Read More
2027: Guguwar haɗaka ta zaburar da Tinubu

2027: Guguwar haɗaka ta zaburar da Tinubu

Daga BAKURA MUHAMMAD Ziyarar bazata da tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya kai wa tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da kuma tagomashi da jirgin haɗakar 'yan siyasa ya ke samu, da alama hakan yana yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu barazanar ɗaukar wasu wajiban matakai, da suka haɗa da yi wa gwamnatinsa garanbawul, da ya haɗa da zubar da wasu cima-zaunen shugabannin hukumomin Gwamnatin Tarayya, da yi wa jam'iyyarsa ta APC canjin shugabanni. Wata majiya makusanciyar tsare-tsaren zaɓen shekarar 2027 da ke Fadar Shugaban ƙasa, wacce ta sakaye bayyanar da kanta, ta ce tun daga wannan lokacin take…
Read More
An ga giftawar Kwankwaso a Villa

An ga giftawar Kwankwaso a Villa

*Raɗe-raɗin komawar Kwankwaso APC ya ƙaru Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Maganganu suna ta yawo kan batun cewa, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, zai koma Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya, musamman a wayewar garin ranar Alhamis bayan da wasu majiyoyi suka shaida cewa, an ga giftawarsa a Fadar Shugaban ƙasa. “Mu na shirin fita daga Fadar Shugaban ƙasa, sai aka ce mana, ‘ga Kwankwaso can ya shigo zai gana da Maigida’” inji wata majiya mai tushe, wacce ta nemi Blueprint Manhaja ta sakaya sunanta. Masu maganganu dai suna cewa, tsohon gwamnan na Kano zai fice daga…
Read More
Ana artabu tsakanin Fulani da Lakurawa a Kebbi

Ana artabu tsakanin Fulani da Lakurawa a Kebbi

*Zarge-zarge sun fara fito wa fili a yankuna Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Rahotanni daga ɓangaren yankin ƙananan hukumomin Arewa da Augie a Jihar Kebbi na nuni da cewa, yanzu haka ana artabu tsakanin ’yan ta’addar Lakurawa da Fulani makiyaya a waɗannan yankunan sanadiyyar shigar burtu da makiyayan ke yi suna kai farmaki a waɗansu ƙauyuka suna kisan mutane a al’ummomi daban-daban. Wani jami'in tsaro da ya ke aikin sintiri a wannan yankin, wanda bai amince a ambaci sunansa ba, ya shaida wa Wakilin Blueprint Manhaja cewa, sau da yawa Lakurawan sukan kashe Fulanin ne, saboda suna kai farmaki suna…
Read More
Ambaliya: Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi jihohi 30

Ambaliya: Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi jihohi 30

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce, za a fuskanci mamakon ruwan sama, wanda zai iya haddasa ambaliyar ruwa a jihohi 30 da Babban Birnin Tarayya Abuja a daminar bana ta 2025. Ministan Albarkatun Ruwa, Mista Joseph Utsev ne bayyana haka a jiya Alhamis a yayin gabatar da hasashen kan ambaliyar ruwa, wanda hukumar da ke kula da rafuka ta ƙasar, NIHSA, ta yi. Jihohin da za su iya fuskantar ambaliyar ruwan sun haɗar da Legas da Ogun da Abia da Ondo da Adamawa da Akwa Ibom da Anambra da Bauchi da Benuwai da Borno da Bayelsa da…
Read More
Kisan ’yan Arewa a Edo ya tada hazo

Kisan ’yan Arewa a Edo ya tada hazo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Bayanai da Blueprint Manhaja ta tattaro daga garin Uromi na nuna cewa, mazauna garin da maƙwabta na tserewa daga garuruwan nasu, saboda zaman ɗar-ɗar da fargabar hare-haren ɗaukar fansa da kuma kamun 'yan sanda. Tun dai bayan kisan wasu maharba kimanin 16, inda wasu rahotannin suka nuna cewa, sun kai 21, matafiya 'yan arewacin ƙasar da 'yan sintiri suka yi a Uromi da ke Jihar Edo suka yi ake ta samun zazzafan martani daga shugabannin yankin da ke ta kiraye-kirayen sai an hukunta waɗanda suka yi wannan aika-aika. "Shaguna sun kasance a rufe, inda…
Read More
Mataimakin Shugaban ƙasa da gwamnoni: Majalisar Wakilai ta janye ƙudirin cire rigar kariya

Mataimakin Shugaban ƙasa da gwamnoni: Majalisar Wakilai ta janye ƙudirin cire rigar kariya

*Ta miƙa ƙudirori 39 ga kwamitin tsarin mulki  Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Wakilai ta soke matakin da ta ɗauka kan ƙudirin gyaran fuska a karatu na biyu na neman cire wa mataimakin shugaban ƙasa, gwamnoni da mataimakansu rigar kariya. Majalisar dai ta ɗauki matakin ne bayan Hon. Julius Ihonbere, Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar, ya gabatar da ƙudiri a ranar Alhamis. Kudirin, wanda ya tsallake karatu na biyu a ranar Larabar da ta gabata, wani ɗan Majalisar Wakilai na jam’iyyar PDP daga Jihar Ribas, Hon. Solomon Bob ne ya ɗauki nauyinsa. Majalisar Wakilai ta soke matakin da…
Read More
Dokar ta-ɓaci a Ribas: Majalisar Dokokin Nijeriya ta sahale wa Tinubu

Dokar ta-ɓaci a Ribas: Majalisar Dokokin Nijeriya ta sahale wa Tinubu

*Bisa doka Tinubu ya yi aiki – Antoni Janar *'Yan adawa, NBA da NLC sun yi fatali da dokar *Za mu bi hanyoyin doka don dawo da haƙƙinmu – Fubara Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dokokin Nijeriya, wacce ta ƙunshi Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai sun goyi bayan ayyana dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a jihar Ribas mai fama da rikicin siyasa. A ranar Talata ne Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Ribad tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Ngozi Odu da 'yan majalisar dokokin jihar Ribas tsawon wata shida sakamakon…
Read More