Ambaliya: Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi jihohi 30

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce, za a fuskanci mamakon ruwan sama, wanda zai iya haddasa ambaliyar ruwa a jihohi 30 da Babban Birnin Tarayya Abuja a daminar bana ta 2025.

Ministan Albarkatun Ruwa, Mista Joseph Utsev ne bayyana haka a jiya Alhamis a yayin gabatar da hasashen kan ambaliyar ruwa, wanda hukumar da ke kula da rafuka ta ƙasar, NIHSA, ta yi.

Jihohin da za su iya fuskantar ambaliyar ruwan sun haɗar da Legas da Ogun da Abia da Ondo da Adamawa da Akwa Ibom da Anambra da Bauchi da Benuwai da Borno da Bayelsa da Kuros Riba.

Sauran su ne Delta da Ebonyi da Edo da Gombe da Imo da Jigawa da Kebbi da Kogi da Kwara da Nasarawa da Neja da Osun da Oyo da Ribas da Sakkwato da Taraba da Yobe da Zamfara da kuma Birnin Tarayya Abuja.

Ministan ya ce, wasu ɓangarori na yankin Kudu maso Kudancin ƙasar za su fuskanci ambaliya ta gaɓar teku, tafkuna da rafuka, inda ya ƙara da cewa, jihohin sun haɗar da Bayelsa da Kuros Riba da Delta da Ribas, yayin da Akwai-Ibom da kuma Edo za su kasance cikin mummunan haɗarin ambaliyar ruwan.

A cewar ministan, ambaliyar ruwa ita ce babbar masifar yanayin da ke ɗaiɗaita mutane da albarkatun ƙasa a Nijeriya sannan kuma sauyin yanayi ne ke ƙara haɗarin afkuwa ambaliyar.

Joseph Utsev ya ce, jihohin da suka haɗa da Abia da Benue da Legas da Bayelsa da Ribas da kuma na daga cikin jihohin da ke cikin haɗarin fuskantar ambaliyar ruwa.

By ukarofi