Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Damaturu
Gwamnatin Jihar Yobe ta bayyana cewa a shirye take wajen karɓar tubabbun mayaƙan Boko Haram waɗanda suka ajiye makamai zuwa cikin al’umma; waɗanda kuma suka samu horon gyaran, tare da inganta halayen su a ƙarƙashin rundunar sojojin Nijeriya ta Operation Safe Corridor (OPSC).
Gwamnan jihar, Mai Mala Buni, ya bayyana hakan a ranar Alhamis, lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar Operation Safe Corridor, dake ƙarkashin Janar Christopher Musa, Babban Hafsan Sojoji (CDS), a babban birnin jihar, dake Damaturu.
Gwamnan, wanda Mataimakinsa, Hon. Idi Gubana ya wakilta, ya ce wannan ziyara ce mai muhimmanci wadda za ta samar da haɗin gwiwa tsakanin jihar da rundunar sojoji don magance matsalar tsaro.
Har wala yau kuma, Gwamna Buni ya bayyana takaicin yadda rikicin ya shafe sama da shekaru 15, tare da sanadiyar laƙume dubban rayukan al’ummar jihar, lalata kadarorin gwamnati da na jama’a haɗi da na jama’a tare da jawo asarar matsugunan al’umma.
Ya ce gwamnatin jihar ta fahimci cewa ba duk yan ƙungiyar ta’addancin ne suka shiga da son rai ba, kuma ta ƙara da cewa akwai damar amfani da wasu matakan da suka dace domin gyara tunani, halayyar waɗanda suka nuna nadama daga cikin mayaƙan.
“Mun yarda cewa wasu an tilasta musu shiga cikin wannan ƙungiya ta yan ta’adda ta hanyar tilastawa ko kuma barazana.
“Kuma idan aka ci gaba da irin wannan ƙoƙarin, za su iya tuba, su kyautata hali da rayuwarsu, su koma cikin al’umma a matsayin yan ƙasa nagari.” In ji Buni.
Gwamnan ya ce, waɗannan masu tada ƙayar bayan 390 waɗanda suka bayyana tubansu, ciki har da yan asalin jihar Yobe 54, za su kammala shirin horaswa na sauya musu tunani tare da kyauta ɗabi’un su (DRR) tsakanin ranar 14 zuwa 19 ga wannan wata na Afrilu.
Ya ce jihar a shirya take, ta ɓangaren Ma’aikatar Ayyukan Jin ƙai, don tabbatar da ingantaccen tsarin sake dawo da tubabbun Boko Haram cikin al’umma.
“Saboda haka ina mai ƙara baiwa Operation Safe Corridor tabbacin cewa gwamnatin jihar Yobe ta himmatu wajen aiwatar da shawarwarin da ta bayar wajen ganin an cimma burin da aka saka a gaba,” In ji Gwamna Buni.
Bugu da ƙari kuma, Gwamnan ya yaba wa Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu bisa ga ƙoƙarin sa da “ingantattun ƙudurorinsa na ganin an kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci tare da aikata manyan laifuka ta hanyoyi daban-daban a faɗin ƙasar nan.”
A nashi ɓangaren, shugaban ɓangaren yiwa tubabbun Boko Haram afuwa (CDS) ya ce Operation Safe Corridor (OPSC) ta samar da wannan tsari ne don tabbatar da cewa akwai waɗanda suke da anniyar tuba da gaske tare da neman afuwa.
Ya ce wasu daga cikin mayaƙan Boko Haram sun yi amfani da garkuwa da suke yi da wasu mutane, su yi musu barazana tare da gurɓata musu tunani da tilasta mu su shiga ƙungiyar, yayin da wannan tsari na yin afuwa da cire musu gurbatattun tunani a ƙarƙashin kulawar DRR.
“Operation Safe Corridor ba shiri ne na ramuwar gayya ba; ya na nufin lalubo sahihan hanyoyin zaman lafiya da sulhu,” in ji Musa, wanda Brigadier-Janar Yusuf Ali ya wakilta.
Haka zalika kuma, Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Operation Safe Corridor, ya ƙara da cewa: “Yawancin waɗanda muke tantancen, su kansu waxanda aka zalunta ne.
“Kuma mun fahimci nadama a fuskokin su tare da kuma sha’awarsu na samun sauyin rayuwa don ci gaba da rayuwa kamar kowa.”
Ya jaddada kira ga al’umma su karɓi tubabbun da zuciya ɗaya don ci gaba da gudanar da rayuwa, ya na mai cewa gyaran tunanin ya na da buƙatar dole ne suma al’umma su tallafa.
Musa ya kuma roƙi gwamnatin jihar Yobe ta tallafa wajen faɗaɗa cibiyoyin gyara tunani, horar da su kan sana’o’i, da samar da kayan aiki don inganta shirin.
