NYEEF ta taya Kwamared Salihu Ɗantata murnar sabon muƙaminsa

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Ƙungiyar inganta rayukan matasan Arewa, wato ‘Northern Youth Empowerment & Enlightenment Forum’ (NYEEF), ta taya Kwamared Salihu Mahmud Ɗantata murna bisa naɗin da aka masa na zama mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga Ƙaramin Ministan Ma’aikatar Ayyuka, Muhammad Bello Goronyo.

A wata takardar taya murna da shugaban ƙungiyar, Kwamared Abubakar Ya’u ya sanya wa hannu a ranar 10 ga Afrilu, ƙungiyar ta bayyana cewa naɗin ya zo ne sakamakon jajircewa, gaskiya da riƙon amana da Ɗantata ke da shi, wanda hakan ya sa ya cancanci wannan matsayin na musamman.

NYEEF ta ce, muƙamin ya nuna irin nasarar da Ɗantata ke samu a aikinsa da kuma yadda ya ke zama abin koyi ga matasa.

Ƙungiyar ta kuma bayyana naɗin a matsayin wata babbar nasara ga Ɗantata da ma ga ɗaukacin mambobin ƙungiyar gami da dukkan matasa masu kishin ci-gaban ƙasa.

Ƙungiyar ta yi addu’ar Allah ya ba shi nasara a sabuwar rawar da zai taka tare da fatan zai kasance ginshiƙi wajen isar da saƙon ma’aikatar zuwa ga al’umma da kuma inganta ayyukan gwamnati.

By Babaji