Da Ɗumi-Ɗumi: Matatar Ɗangote ta sake rage farashin fetur

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A yau ne Matatar mai ta Ɗangote ta mayar da farashin litar fetur zuwa N865.

Hakan ya nuna an samu ragin N15 daga N880 da aka saya a ranar Laraba.

Lamarin ya biyo bayan dakatar da tsarin cinikin ɗanyen mai da Naira da gwamnatin Tarayya ta yi a baya.

Tuni ƴan kasuwar mai da suka haɗa da Kamfanin MRS suka fara dakon fetur daga matatar, wadda ke fitar da ganga 650,000 a kullum.

A baya ne matatar ta rage farashin zuwa N815, wanda shi ne ragi karo na uku a cikin shekarar 2025.

By Babaji