
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Haɗaka ta Kula da bada Gurbin karatu ga ɗalibai (JAMB), ta ce N30,000 kowane ɗaya daga cikin ɗalibai 180 ya biya ta shafinta da aka yi wa tarko don samun damar yin satar amsa a yayin gudanar da jarrabawar UTME ta shekarar 2025.
A lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a yayin sanya ido kan jarrabawar Mock UTME a Hedikwatar hukumar dake Abuja, Rajistiranta, Farfesa Ishaq Olanrewaju Oloyede, ya ce za a hukunta duk wanda aka samu da hannu a aikata laifin ta hanyar ƙwace masu UTME ko kuma DE, wato ‘Direct Entry’ bisa ƙoƙarin satar amsa.
Farfesan ya kuma ce, aƙalla ɗalibai 211,000 ne suka rubuta jarrabawar Mock UTME a cibiyoyin da ta ware na CBT a faɗin Nijeriya, ya na mai cewa za a fitar da sakamakon jarrabawar a ranar Juma’a, 11 ga watan Afrilun 2025.
Ya bayyana cewa, za a yi amfani da jarrabawar ne wajen gyara duk wata matsala game da bayanan da ke kan na’ura a yayin da ake fuskantar jarrabawar UTME da za a yi a ranar 25 ga Afrilu.
Kazalika, Farfesa Oloyede ya ce, kamar yadda ɗaliban suke ƙara wayewa, haka su ma suke cigaba da samun hanyoyin warware matsalolin da ka iya haifar da tsaiko a yayin gudanar da kowacce gaɓa ta aikinsu.
Ya jaddada cewa, amintacciyar hanyar da ake cin jarrabawa da ita kaɗai, ita ce yin karatu sosai, ya na mai ikirarin hukunta duk waɗanda aka samu da yunƙurin satar jarrabawa.
