Jami’an tsaro sun kuɓutar da mutane 10 daga hannun ‘yan ta’adda a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Haɗin gwiwa na jami’an ‘yan sanda da jami’an tsaro na al’umma CWC sun sami nasarar kuɓutar da mutane 10 daga hannun ‘yan ta’adda a ƙauyen Gidan Make da ke ƙaramar hukumar Musawa.

Bayanin haka na ƙunshe ne a wata takardar sanarwa ɗauke da sa hannun Kwamishinan cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa.

Ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun kai hare hare ne a ƙauyukan Kirkiro, Karbi da Gidan Marke sai dai basu sami nasarar tafiya da kowa ba,bayan da jami’an tsaro suka Kawo wa al’ummar ƙauyukan ɗauki .

Jami’an tsaron ƙarƙashin DPO na Musawa suka fatattaki ‘yan ta’addan bayan ɗauki ba daɗi da ‘yan bindigan a ƙauyen Gidan Marke.

Dr Ɗanmusa ya ƙara da cewa jami’an tsaron sun sami nasarar kuɓutar da mutanen su 10 da kashe ɗaya gada cikin ‘yan bindigan wasu da yawa cikin su sun gudu suna ɗauke da manyan raunuka.

Tuni jami’an tsaron suka miƙa mutanen da aka kuɓutar ga iyalan su.

Kwamishina ya jaddada ƙudirin gwamnatin Dikko Raɗɗa na kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar”kuma zamu cigaba da yaƙar waɗannan miyagun mutane har sai mun kakkaɓe su a jihar da yardar Allah”inji Ɗanmusa.

Ya sanar da cewa gwamna Dikko Raɗɗa ya yabawa haɗin gwiwar jami’an tsaron kan yadda suke haɗa kan su da nuna ƙwarewa da kuma ƙwazo wajen tunkarar ta’addanci a jihar.

Kwamishinan sai yayi kira ga al’ummar yankunan da ake fama da ta’adanci da su taimakawa jami’an tsaro wajen bada sahihan bayanai na sirri kan maɓoyan ‘yan ta’adda a yankunan.

By ukarofi