*Bisa doka Tinubu ya yi aiki – Antoni Janar
*’Yan adawa, NBA da NLC sun yi fatali da dokar
*Za mu bi hanyoyin doka don dawo da haƙƙinmu – Fubara
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar Dokokin Nijeriya, wacce ta ƙunshi Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai sun goyi bayan ayyana dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a jihar Ribas mai fama da rikicin siyasa.
A ranar Talata ne Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Ribad tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Ngozi Odu da ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas tsawon wata shida sakamakon rikicin da jihar ta faɗa.
Kwana biyu bayan ɗaukan matakin ne Tinubu ya aike da takarda zuwa ga majalisun guda biyu, inda yake neman amincewarsu ga matakin da ya ɗauka.
A zaman da majalisar wakilai ta yi jiya Alhamis, kakakin majalisar wakilan, Tajuddeen Abbas ya karanto wasiƙar da Tinubu ya aike masu.
‘Yan majalisar sun amince, da gagarumin rinjaye, matakin Tinubu na ayyana dokar ta-ɓacin.
A cewar kakakin majalisar, ‘yan majalisa 240 ne suka halarci zaman, hakan na nufin an samu adadin ‘yan majalisar da ake buƙata wajen amincewa da duka wani ƙudiri.
Matakin Shugaba Tinubu dai ya yamutsa hazo a Nijeriya inda al’ummar ƙasar ke tsokaci game da hurumi ko rashin hurumin shugaban ƙasar ya ɗauki irin wannan matsaya.
Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Ribas a wani jawabi da ya yi ta kafafen talabijin na ƙasar, bayan rikita-rikitar siyasa da jihar ta daɗe tana fama da shi.
A cikin jawabin nasa, Tinubu ya yi nuni da yadda aka rushe ginin majalisar dokokin jihar watanni 18 da suka gabata, wadda aka kasa sake gina ta har zuwa wannan lokaci.
“Jihar ta tsaya cik tun bayan ɓarkewar rikicin siyasar inda aka tauye wa al’ummar jihar haƙƙinsu na cin moriyar mulkin dimokuraɗiyya.
”Na yi iyakar bakin ƙoƙarina wajen ganin yadda za a magance matsalar to amma duka ɓangarorin sun yi watsi da yunƙurin.”
Tinubu ya bayyana cewa babu wani shugaban ƙasa nagari da zai zura ido yana kallon abin da ke faruwa ba tare da bin matakan da kundin tsarin mulki ya tanada ba wajen ganin an shawo kan matsalar ta jihar Ribas.
A cikin jawabin da ya gabatar ta kafafen talabijin na ƙasar, Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce: ”Bayan nazari kan halin da ake ciki a jihar Ribas, ya zama wajibi na yi amfani da sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999.
“A kan haka, na ayyana dokar ta-ɓaci daga yau 18 ga watan Maris, 2025.
“Da wannan bayani, gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Mrs Ngozi Odu da kuma dukkanin zaɓaɓbun ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas, an dakatar da su na wata shida, a matakin farko.”
Gwamnan jihar Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar sun kasa samun fahimtar juna kusan tun bayan hawansa kan mulki, duk kuwa da hukunce-hukunce da kotu ta zartar.
Haka nan shugaban ƙasar ya bayyana cewa wasu mutane daga ɓangarori daban-daban su ma sun yi nasu ƙoƙarin amma an kasa samun mafita.
”A yanzu ta tabbata babu wata sahihiyar gwamnati a jihar Ribas,” inji Shugaba Tinubu.
A cikin jawabin da ya gabatar, shugaban na Nijeriya Bola Tinubu ya bayyana sunan ɓice Admiral Ibokette Ibas, mai ritaya a matsayin wanda zai jagorancin al’amuran jihar tsawon lokacin da dokar za ta yi aiki.
“A halin yanzu, na naɗa ɓice Admiran Ibokette Ibas a matsayin wanda zai gudanar da lamurran jihar, domin amfanin al’ummar jihar,” inji Tinubu.
Sai dai a cikin jawabin nasa, Tinubu ya bayyana cewa wannan doka da ya ƙaƙaba ba ta shafi ɓangaren shari’a na jihar ba.
Tinubu ya ce a tsawon lokacin da Ibas zai jagoranci jihar, ba zai samar da wata doka ba, sai dai zai iya samar da wasu ƙa’idoji waɗanda za su buƙaci amincewar Majalisar Zartarwar Tarayya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, dakataccen gwamnan, Siminalayi Fubara ya ce tun hawansa mulki, ya yi ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma kawo cigaba a jihar, sai dai ‘yan majalisar dokokin jihar suna ta kawo cikas ga ƙoƙarin nasa.
Fubara ya ce dukkanin abubuwan da ya yi da matakan da ya ɗauka ya yi su ne bisa rantsuwar da ya sha na kama aiki, inda ya ce hakan ne ya sa bayan da Shugaba Tinubu ya shiga tsakani, ya yi gaggawar aiwatar da yarjejeniyar da aka amince ciki har da dawo da kwamishinonin da suka ajiye aiki.
Ya kuma ce ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen bin hukuncin kotun ƙoli domin dawo da zaman lafiya a jihar, sai dai a cewarsa, a kowane mataki ƙoƙarinsa ya gamu da cikas daga ɓangaren majalisar dokokin jihar.
Sanarwar ta ƙara da cewa duk da rikicin siyasar da ake yi, gwamnan ya ci gaba da gudanar da gwamnati yadda ya kamata, inda ya ce ana biyan ma’aikata albashinsu kuma an ƙaddamar da muhimman ayyukan cigaba a jihar.
Fubara ya buƙaci ‘yan ƙasar su ci gaba da kasancewa masu biyayya ga dokar ƙasa, inda ya ce za su ci gaba da tuntuɓar waɗanda suka dace wajen tabbatar da ɗorewar dimukraɗiyya a jihar, kuma jihar ta ci gaba da bunƙasa.
A ɓangare guda kuma, ƙungiyoyi da masu ruwa da tsaki a sha’anin mulki a Nijeriya, suna ta tofa albarkacin bakinsu kan wannan dambarwa, inda suke ganin cewa babu wata dokar ƙasa da ta ba Shugaban ƙasa damar tsige zaɓaɓɓen gwamna ko wani zaɓaɓɓe a kowane mataki.
ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta soki matakin da shugaban ya ɗauka na ayyana dokar ta-ɓaci da kuma cire Gwamna Similanayi Fubara.
Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Shugaban NBA, Mazi Afam Osigwe (SAN), ya ce a ƙarƙashin Kundin Tsarin Mulki, shugaban ƙasar ba shi da ikon tsige zaɓaɓɓen gwamna bayan ayyana dokar-ta ɓaci a jiharsa.
“Saboda haka duk wani matakin da ya saɓa wa tsarin mulkin dimokuraɗiyya wanda kuma ya keta haddin cin gashin kan gwamnatocin jihohi,” inji shi.
A kan haka ne ƙungiyar Lauyoyin ta buƙaci Majalisar Dokoki ta ƙasa da ta yi watsi da duk wani yunƙuri na tsige Gwamnan Jihar Ribas da sauran zaɓaɓɓun jami’an da aka yi ba bisa ƙa’ida ba.
“Dole ne ya zamanto ayyana dokar ta-ɓaci ta dogara da ƙwararan dalilai na tsarin mulki, ba wai wata manufa ta siyasa ba.”
NBA ta yi gargaɗin cewa akwai barazana mai hatsarin gaske ta dakatar da zaɓaɓɓun jami’an da ke ƙarƙashin dokar ta-ɓaci, wanda zai iya kawo wa dimokuraɗiyya cikas na buɗe ƙofar tsige zaɓaɓɓun gwamnatoci a nan gaba.
ƙungiyar ta yi kiran cewa duk wani mataki da aka ɗauka a Jihar Ribas ya bi ƙa’idojin tsarin mulki da kuma ƙa’idojin dimokuraɗiyyar Nijeriya.
Kazalika, ta buƙaci duk masu ruwa da tsaki da suka haɗa da ɓangaren shari’a, da ƙungiyoyin farar hula, da ƙasashen duniya da su sanya ido sosai kan halin da ake ciki a Jihar Ribas domin daƙile duk wani yunƙuri da ke yi wa masu riƙe da madafun iko katsalandan ba bisa ƙa’ida ba.
Haka su kuma ƙungiyiyin ƙwadagon Nijeriya NLC da TUC sun buƙaci Tinubu ne ya mayar da gwamnan Ribas kan muƙaminsa nan take
Kungiyoyin sun yi kakkausan Allah wadai da abin da suka bayyana a matsayin saɓa doka da Shugaba Tinubu ya yi, wajen kafa dokar ta-ɓaci da dakatar da gwamnan jihar da mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin jihar.
ƙungiyoyin sun ce matakin ya saɓa wa tanadin sashe na biyu, da sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima, kuma ya zama cin zarafi ga ikon zartarwa.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ƙungiyoyin suka fitar ranar Larabar nan, kwana guda bayan Shugaba Tinubu ya sanar da matakin nasa, da ya haifar da ce-ce-ku-ce a faɗin ƙasar.
Sanarwar ta buƙaci shugaban ƙasar ya gaggauta janye sanarwar da ya bayar, da ka iya ɗora ƙasar a kan tubalin saɓa wa doka a nan gaba.
Gwamnonin Jam’iyyar PDP sun buƙaci Shugaba Tinubu da ya janye dakatarwar da ya yi wa gwamnan na Ribas.
ƙungiyar Gwamnonin ta PDP ta bayyana dakatarwar da aka yi wa Fubara a matsayin “babban kuskure” sannan mummunan mataki ne da zai haifar da koma-baya.”
Cikin wata sanarwa ranar Laraba, Bala Mohammed wanda shi ne Gwamnan Jihar Bauchi kuma Shugaban ƙungiyar Gwamnonin PDP, ya ce ayyana dokar ta-ɓacin a Ribas abin damuwa ne kan makomar jihar.
Gwamna Bala Muhammad ya ce jan baki ya yi shiru da Tinubu ya yi kan rawar da Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja ke takawa a rikicin siyasar na Ribas kamar ba shi dama ce ya yi kiɗinsa kuma ya yi rawarsa.
Ya ce “Wike ya zama doka saboda yana yin abin da kake so. Yanzu mun sani. Wannan sam babu dattako, an nuna son kai da kuma rarraba kawuna,” inji sanarwar.
ƙungiyar gwamnonin ta PDP ta ce matakin ƙarara barazana ce ga dimukraɗiyyar Nijeriya sannan zai ƙara rura wutar rikici a ƙasar tare da ƙara janyo rashin yarda da lalata tattalin arziki da kuma zaman lafiyar ƙasa baki ɗaya.
ɗan takarar Shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, da na Labour, Peter Obi da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufai sun yi fatali da matakin Shugaban Nijeria na ƙaƙaba dokar ta-ɓaci a jihar Ribas.
El-Rufai da sauran jagororin jam’iyyun hamayya sun buƙaci Majalisar dokokin Nijeriya ta yi watsi da ƙudirin.
Shi ma ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023 ƙarƙashin inuwar PDP, Atiku Abubakar, a jawabin da ya yi ranar Alhamis, ya zargi Tinubu da nuna ɓangaranci.
Atiku Abubakar ya kuma nemi Shugaba Tinubu da ya janye matakin wanda ba ya bisa kundin tsarin mulkin ƙasa sannan ya maido da zaɓaɓɓen gwamna da mataimakiyarsa da sauran mutanen da aka dakatar kan kujerarsu.
A cewarsa sun yi tur da matakin sannan sun yi kira ga ‘yan Nijeriya da su soki ƙudirin wanda ya saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma dimokraɗiyya.
Dr. Reuben Abati, tsohon mai taimakawa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan kan harkokin yaɗa labarai, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cancanci a tsige shi saboda ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Ribas.
Abati ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata a yayin shirin safiya a gidan Talabijin na Arise, inda ya ce matakin na Tinubu ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Nijeriya, musamman sashi na 305, wanda ya bayyana tsarin doka na ayyana dokar ta-ɓaci.
“Ba za a iya tsige gwamna da shelar shugaban Nijeriya ba,” Abati ya bayyana, yana mai jaddada cewa Tinubu ba shi da ikon da tsarin mulki ya ba shi na rusa majalisar dokokin jihar Ribas ko kuma naɗa wani mai gudanar da mulki.”
Kusan sa’o’i ashirin da huɗu bayan ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Ribas, gwamnatin tarayya a ranar Laraba ta ce za ta saki kason kuɗin jihar ga kantoman riƙo, ɓice Admiral Ibok Ibas (mai ritaya), wanda tsohon babban hafsan sojin ruwa ne.
Haka kuma ta ce tsoma bakin da Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ya dace da nufin kaucewa wata tangarɗa a jihar.
Kuma a duk wannan, gwamnatin ta kuma yi watsi da cece-kucen jama’a kan tsohon gwamnan jihar kuma ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, inda ta ce ba shi da wata rawa a rikicin siyasar da ya kai ga kafa dokar ta-ɓaci.
Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, SAN, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa a Abuja.
“Yanzu, yaushe kuke ganin ya kamata shi (Shugaba Tinubu) ya shigo? Har sai an lalata komai? Bana jin haka.
“Ina ganin Shugaban ƙasa ya ɗauki matakin da ya dace, ya ba da dama ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa su gyara, kafin lokacin, sai da ya tattara su, kuma ya yi ƙoƙarin shiga tsakani,” inji shi.
Kazalika Ministan shari’an ya yi zargin cewa Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas ya jagoranci ‘yan bindiga ta wayar tarho domin fasa bututun mai a jihar.
Fagbemi, wanda ya gana da shugaban ƙasar a fadar shugaban ƙasa a ranar Larabar da ta gabata, ya shaida wa manema labarai na fadar gwamnati cewa, Fubara ya zama mai laifi ne a lokacin da ya sanya ‘yan bindiga a jihar cikin shirin ko ta kwana na barazanar tsige shi.
A cewar AGF, da gangan Gwamnan bai yi wani abu da zai hana tsagerun ɗaukar matakin ɓarna a kan muhimman ababen more rayuwa na ƙasa ba.
“Bari mu ce ba daidai ba ne, shin ya fito ne domin ya musunta su? Amsar ita ce a’a, kuma bayan mako guda, sai suka koma aiki, sai ka ga ko ka shaida fasa bututun mai.”
Ya ce ga al’ummar da ta dogara kusan kacokan akan man fetur, duk wanda ya taɓa bututun mai, shi ba maƙiyin Ribas ne kaɗai ba, har ma da Nijeriya.
Idan za a iya tunawa, tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a Nijeriya a shekarar 1999, Tinubu ne shugaban ƙasa na uku da ya yi amfani da sashe na 305 na kundin tsarin mulkin ƙasar. Tsohon Shugaban ƙasa Olusegun ya yi sau biyu, a Filato (2004) da Ekiti (2006) a lokacin mulkinsa na shekara takwas.
Tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan shi ma ya bi irin wannan hanya a jihohin Adamawa, Yobe da Borno a lokacin da ake fama da tashe-tashen hankula a shekarar 2013.
Amma a lokacin Bola Tinubu shi ne jagoran rusasshiyar Action Congress of Nigeria (ACN) ya dinga ƙalubalantar matakin tare da yin watsi da shi bayan ayyana matakin a matsayin “hanyar da ke da haɗari a harkar shugabanci.”
Da yake sukar Jonathan, Tinubu ya ce matakin na da alaƙa da siyasa.
Siyasar jihar ta Ribas ta damalmale ne tun bayan da rashin jituwa ya ɓulla tsakanin gwamnan jihar Siminalayi Fubara da magabacinsa, ministan birnin tarayyar Nijeriya, Nyesom Wike.
Lamarin ya kai ga cewa ‘yan majalisar dokokin jihar masu biyayya ga tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike sun yi barazanar tsige Gwamna Fubara.
