
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta ce, gwamantin Shugaba Bola Tinubu ta samar wa al’ummar Nijeriya sauƙi a harkokinsu na yau da kullum.
Gwamnatin ta kuma yi sanadin zuba jarin da adadinsa ya kai Dala biliyan 14 daga ƙasar Indiya a ɓangarori da dama da cinikin Dala biliyan 8 na Indorama da kuma zuba jarin Dala biliyan 3.5 a tashar ƙarafuna a Jihar Akwa-Ibom.
An bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai na ma’aikatu da ya haɗa da Ministocin harkokin cikin gida da na waje, Olubunmi Tunji-Ojo da Yusuf Tuggar a Abuja.
Ministan Cikin gida, Tunji-Ojo, ya ce gwamnatin ta sauƙaƙe wa al’umma hanyoyin mallakar fasfo da bunƙasa tsaro akan iyakoki da samar da yanayi mai kyau ga tsaro na ɓangarori daban-daban.

Ya bada misali da inganta ayyukan Hukumar Shige-da-fice inda aka mayar da tsarin amince wa biza ya zama na bai-ɗaya, sauƙaƙe hanyoyin bada fasfo da daidaita shi da tsarin ƙasashen duniya da sauran su.
Ya kuma ce, ta samar da cibiyoyin kula da iyakoki a Nijeriya na ƙarnin 21 ta yadda babu wani mai laifi da zai kutso ƙasar ba tare da an kama shi ba.
Ya ƙara da cewa, gwamanti na iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta bai wa manoma kariya ta yadda za a samu tsaro ga samar da wadataccen abinci ga al’umma, inda ya ce ta horar da jami’ai 10,000 da za su riƙa zuwa gonaki don bada kariya ga manoma.
A nasa jawabin, Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce ma’aikatarsu ta samar da hanyar samun zuba jari na Dala biliyan 14 daga ƙasar Indiya haka kuma Nijeriya ta ƙulla yarjejeniyoyi na MoUs da ƙasashe goma akan alaƙar harkoki daban-daban.
Ƙasashen sune; Jamus, Saudiyya, Chana, Equatorial Guinea, Faransa, Cuba, Ƙatar, Birtaniya, Indiya da Brazil.
Ya bada misali da karɓo fursunoni ƴan Nijeriya da gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi waɗanda aka tsare su bisa zalunci na tsawon shekaru a ƙasashe da dama.
