Ba mu umarci a sako Nnamdi Kanu ba – NJC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar Alƙalan Nijeriya (NJC), ta musanta batun da ke yawo na cewa Alƙalin Alƙalai, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun ta umarci a gaggauta sako Shugaban ƙungiyar fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu da aka tsare da mayar da shi ƙasar Kenya.

Mataimakin Daraktan yaɗa labarai na NJC, Kemi Ogedengbe ya faɗa wa manema labarai hakan a Abuja.

A ranar Juma’a ne za a sake gurfanar da Kanu a gaban Babbar Kotun Tarayya, inda Alƙali James Omotosho zai cigaba da sauraron ƙarar, bayan da Alƙali Binta Nyako ta tsame hannunta daga ciki saboda Kanu ya zarge ta da ɗaukar ɓangare a lokacin da ta ke hukunci akan ƙarar da aka shigar akansa a baya.

Saidai, a yayin kare batun, NJC ta ce ba ta bada umarnin sako shi ba, kuma babu abinda ya shafe ta da ƙarar Kanu.

Ta ƙaryata rahoton da ke nuna hakan da cewa marubucin ya yi haka ne bisa kintace, ta na mai cewa babu inda ta faɗi hakan.

Haka kuma Alƙali Kekere-Ekun ba ta yi aike na musamman ga gwamantin ƙasar Kenya ba na bada haƙuri kan kama Kanu ko maka shi a kotu.

Don haka ne NJC ta yi kira ga al’umma da su ƙaurace tare da yin watsi da labarin na ƙarya.

By Babaji