Tare da ALI ABUBAKAR SADIK
Sakamakon tambaya da wani ya yi, biyo bayan rubutun aure da saki a fim da na yi jiya, cewar to wai ta ina ma ita harkar Fim ta sami wani halasci daga ƙurani, Hadisi, ko ijtihadin Malamai? Sai na ga ya kamata na bada amsar tambayar tasa domin mahimmancinta, kuma a gane cewa shin a mahangar musulunci, shi kansa film din halal ne ko Haram?
Abu na farko da zamu fara fahimta shine Allah ya ce mana
Q6:38 “…Ba mu yi sakacin barin komai ba cikin littafi (ƙuran)”
Wato ƙurani ya zo da duk wani hukunci, halal ko Haram, a kan duk wani abu da Allah ya ke so, ko wanda baya so. Sai dai kawai a cikin rahamar Allah, ya bar wasu abubuwa da bai ce komai ba a kansu, dalili kuwa shine a fadarsa cewa
ƙ5:101 “Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku yi tambaya ga abubuwa, idan an bayyana muku (hukuncinsu) su ɓãta muku rai. Kuma idan kuka yi tambaya a gare su a lõkacin da ake saukar da Alƙur’ãni, zã a bayyana maku. Allah Yã yãfe laifi daga gare su, Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri”
To amma kuma fa ba komai ne karara ba, yadda da ka bude ƙurani za ka gan shi. Malamai tun asali na amfani da kamanta wani hukunci da ya zo karara a nassi, wajen yin hukuncin wani abu boyayye. Wato kyaukkyawan misali a nan shine na wanda ƙurtubi ya ruwaito a tafsirinsa inda wani ya zo wajen Umar Dan Khattab ya ce “An ce akwai komai a cikin ƙurani…ina son a gaya min yadda ake gurasa a ƙurani. Sai Umar ya ce aje azo masa da mai yin gurasa. Ya umarci mai yin gurasa ta koyawa mutumin. Sai mutumin ya ce “Ni fa daga cikin ƙurani na ke so na gani yadda ake yi” sai Umar ya ce masa “Ga abinda ƙurani ya umarce mu” Q16:43 “Sai ku tambayi mutanen ambato, idan ba ku sani ba”
Don haka idan baka ga wani abu a ƙurani ba, ko dai ya na cikin ajin da Allah ya barwa mutane zabi, ko kuma iliminka ne ya gaza ganewa.
Shin, za mu iya zakulo halasci ko haramcin Fim a ƙurani da Hadisi? Kwarai kuwa, domin Fim ya fado a sashen da ake kira da fasaha (Arts) wadda Dan Adam kadai cikin halittu, Allah ya huwacewa wannan fikira, wadda ta kunshi waka, film, zane-zane da sauransu. Cikin hikimar Allah da sanin mahimmancin wannan fanni, sai ya saukar da sura guda sukutum wadda ya sanyawa suna “Shu’ara” (Mawaka) saboda girman fasaha (arts gaba daya, wato waka, film, zane-zane da sauransu) wanda asalin kalmar ta faro daga Shi’ir wadda a larabci take nufin kirkira ta yin tunani da basira (imagination).
A wannan sura sai Allah ya ce, Q26:224 “Kuma mawaka (poets), halakakku ne ke binsu”
Wannan aya ta tayar da hankali mawakan sahabbai irinsu Abdullah bin Rawaha, Hassan Bn Thabit da Ka’ab Bn Malik. Wanda su ka dunguma su ka tafi wajen Annabi hankalinsu a tashe su na kuka saboda ganin kamar Allah ya la’anci waka da masu yinta. Sai Annabi ya kwantar musu da hankali inda ya ce, su duba ayar da ta biyo bayanta ta, wato: Q26: 227 “Face wadanda su ka yi Imani Kuma suka aikata ayyuka na kwarai, su ka ambaci Allah da yawa”
Wadancan manyan sahabbai sun sami nutsuwa da wannan fatawa ta Manzo wadda ya sake jaddadawa, kamar yadda aka ruwaito a Fathul Bari inda Abu Ya’la ya ruwaito daga Dan Umar cewa Manzon Allah (SAW) Ya ce ‘Waka kirkira ce. Idan lafazan cikinta masu kyau ne, masu amfani, to Mai kyau ce, idan Kuma lafazanta mara sa kyau ne, na sabo, to bata da kyau” Kuma ba za mu manta yadda Annabi ya sha maraba lale da wakar “Dala’al badaru alaina” ranar da ya iso Madina ba.
Bukhari ya ruwaito Aisha na rubuta wakoki. Ya kuma ruwaito Annabi ya bar mata da yara na shan shagalin sallah (wake-wake da kade-kade) har Aisha na lekawa daga cikin gida ta taga. Sahabbai da tabi’ai da dama sun yi wakoki. Muna da sha’irai iri iri a yanzu.
To waka ita ce a wancan lokaci tamkar yadda Fim ya ke a yanzu. Fasaha (Arts) na cikin manyan baiwa da Allah ya baiwa Dan Adam shi kadai, don haka kamar komai akwai nagari da mugu a ciki. Hatta Annabi an yi Fim dinsa “The message” sannan an yi na Annabi Isa, Musa da Ibrahim. Fim halal ne, amma haramci na iya shigowa cikinsa. Kasashen Musulmi irinsu Egypt da Turkiya sun assasa mutanensu wajen tallafawa harkar fina-finai.
Waka, Film, Computer, Wayar hannu, ilimin Boko da duk wani abu irinsu da ke fitar da fikira da basira ta Dan Adam, halal ne, sai dai komai ana iya amfani da shi wajen haramci. A wayarka, kana iya sauraren karatun ƙurani ko binciken hadisai, yin wa’azi, wani kuma na iya shagala da kallon kwallo ko hotunan batsa. Yayin da wani ke tura gudunmuwa ga Yan gudun hijira, wani na can na washe asusun bankin wasu mutanen.
A yanzu, babu wani makami da Dan Adam ya ke da shi irin na Fim wajen aika sako. Mu na gani a gabanmu yadda Amurka ta mamaye duniya a zahiri da tunani, ta hanyar amfani da Hollywood. Fim ya zama kashin bayan fasahar kere-kere yadda aka sami gaggawar habakar ci gaba a Duniya sakamakonsa. Mun ga yadda aka yi amfani da Fim wajen sace tunanin mutane, yadda kasashen Duniya ba shiri su ka rungumi dimokuradiya da jari hujja, abinda ya zama nakasu gare mu. Mu na gani yadda luwadi/madigo da mulhidanci ke fantsama a Duniya kamar wutar daji a yanzu, duk ta hanyar Fim. Wato Fim kamar komai bai iya kaucewa tsarin da Allah ya gina Dan Adam da shi na…”Wa hadainahu, najdain”
Dole mu rungumi wannan fasaha ko don yakar munanan abubuwa, ballantana hanya ce da za ta iya gaggauta yaduwar alheri da arziki da wayewa irin ta musulunci idan mun so. Wajibi ne sai Malamai, Attajirai da gwamnatoci sun bada gudunmuwar da ake bukata kafin Fim ya yi mana tasirin da ya kamata, kamar yadda muke gani a kasashe irinsu Turkiya da Misra a yanzu. Lokaci dai, ba wanda ya taba jira, don haka ba zai fara daga kanmu ba.
A sha ruwa lafiya.
Sadiƙ marubuci ne kuma manazarci, sannan mazaunin Kano
