*Ƙudirin ya tsallake karatu na biyu
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ƙudirin da zai yi wa dokar zaɓe ta 2022 kwaskwarima, domin sanya wa ‘yan Nijeriyar da suka kai shekarun kaɗa ƙuri’a dole ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai.
Shugaban majalisar, Tajjudeen Abbas, da Daniel Ago ne suka ɗauki nauyin wannan ƙudurin dokar.
Da yake jagorantar muhawarar yayin zaman majalisar a ranar Alhamis, Ago ya ce ƙudirin na da nufin ƙarfafa gwiwar ‘yan ƙasa a cikin tsarin zaɓe, tare da lura da cewa za a magance rashin jin daɗin masu kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka idan ƙudirin ya daidaita tsarin majalisar.
Ko da yake ƙudurin dokar ya tsallake karatu na biyu, ɗan jam’iyyar PDP daga jihar Akwa Ibom, Mark Esset, ya ce kafa dokar da za ta tilastawa ‘yan Nijeriya kaɗa ƙuri’a bai isa ya tsaftace tsarin zaɓe ba.
“Kada mu sanya wani abu a kan komai, idan har ‘yan ƙasa sun yi watsi da tsarin zaɓe, akwai ayyuka da yawa da ya kamata a yi.
“Yawancin ‘yan Nijeriya ba sa kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓe, saboda sun yi imanin cewa ƙuri’unsu ba za ta ƙirga ba, idan har sai mun kafa dokar da za ta tilastawa kaɗa ƙuri’a, mu ma mu sanya wani ya sa ƙuri’unsu ta ƙirgu,” inji shi.
Wasu ‘yan majalisar dai sun yi zargin cewa ‘yan ƙasar sun yi watsi da tsarin kaɗa ƙuri’a, tare da nuna shakku kan sahihancin rajistar masu kaɗa ƙuri’a.
Hakazalika, an zartas da ƙudirin dokar da za ta yi wa dokar ƙwadago kwaskwarima, domin ƙara wa’adin hutun mata masu aiki zuwa watanni shida a majalisar wakilai. Hon Chike Okafor (Okigwe ta Kudu/Imo/APC) wanda ya ɗauki nauyin ƙudirin dokar ya tilasta masa sauka daga muƙaminsa bayan da ‘yan majalisar da suka haɗa da mata suka yi muhawara akai.
‘Yan majalisar sun ce ƙara wa’adin hutun haihuwa daga watanni uku zuwa shida zai jefa mata cikin halin ƙunci domin masu ɗaukar ma’aikata za su yi taka-tsan-tsan wajen ɗaukar su aiki.
A halin da ake ciki, Majalisar Dattawa ta tsallake karatu na biyu a kan ƙudirin dokar kafa hukumar yaƙi da cutar zazzaɓin cizon sauro ta ƙasa (NAME) a wani mataki na gaggawa na yaƙi da cutar zazzaɓin cizon sauro, cutar da ke haddasa mutuwar mutane sama da 184,000 duk shekara a ƙasar.
ƙudurin dokar wanda Sanata Ned Munir Nwoko (Delta ta Arewa) ya ɗauki nauyi an fara gabatar da shi ne a ranar 28 ga watan Nuwamba, 2023, amma yanzu an sake dawo da shi tare da sake fasalin taken da kuma mayar da hankali sosai don nuna abin da ɗan majalisar ya bayyana a matsayin gaggawa na ƙasa.
Da yake jagorantar muhawarar, Sanata Nwoko, ya yi tsokaci kan rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya ta 2024, wanda ya nuna cewa, Afirka na samun asarar rayuka kusan 600,000 a duk shekara, inda Nijeriya ke da nauyi mafi girma a duniya.
“Malaria ba batun lafiyar jama’a ba ne kawai, matsala ce ta tsarin aiki, yana ba da gudummawar kashi 11 na mace-macen mata a Nijeriya kuma yana haifar da zubar da ciki, haihuwa da mutuwa da kuma rashin lafiya mai tsanani,” inji shi.
‘Yan majalisar sun bayar da goyon baya sosai ga ƙudurin yana mai jaddada buƙatar samar da tsarin haɗin gwiwa don magance matsalar zazzaɓin cizon sauro da kuma samar da alluran rigakafin cutar zazzaɓin cizon sauro don rage yawan mace-macen da ake samu tare da tabbatar da ɗaukar matakin da ya dace kan ɗaya daga cikin cututtukan da ke kashe mutane a ƙasar.
An miƙa ƙudirin dokar da ta ƙara karatu na biyu zuwa ga kwamitin kula da lafiya don bayar da rahoto nan da makonni huɗu.
