Kisan ’yan Arewa a Edo ya tada hazo

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Bayanai da Blueprint Manhaja ta tattaro daga garin Uromi na nuna cewa, mazauna garin da maƙwabta na tserewa daga garuruwan nasu, saboda zaman ɗar-ɗar da fargabar hare-haren ɗaukar fansa da kuma kamun ‘yan sanda.

Tun dai bayan kisan wasu maharba kimanin 16, inda wasu rahotannin suka nuna cewa, sun kai 21, matafiya ‘yan arewacin ƙasar da ‘yan sintiri suka yi a Uromi da ke Jihar Edo suka yi ake ta samun zazzafan martani daga shugabannin yankin da ke ta kiraye-kirayen sai an hukunta waɗanda suka yi wannan aika-aika.

“Shaguna sun kasance a rufe, inda wasu bayanai ke nuna cewa wasu mazauna garin na barin wurin saboda tsoron abin da zai faru bayan kisan gillar da ta faru a ranar Alhamis,” a cewar shugaban matasan arewacin Nijeriya mazauna garin na Uromi , Babangida SBJ Yawuri ya ce mazauna wurin na cikin fargaba.

“Yayin da da dama daga ‘yan asalain garin ke tsoron shiga kasuwar ‘yan arewacin garin. Saboda ganin da suka yi an ɗauki mataki ƙwaƙƙwara, inji duk irin abin da suke yi wa Bahaushe ba a taɓa samun ɗaukar mataki kamar irin wannan ba,” inji Babangida.

Tuni dai gwamnan na jihar Edo, Monday Okpebholo ya kai ziyara jihar Kano, inda maharan suka fito, inda ya kuma ya ɗauki alƙawarin biyan diyya ga maharban da aka kashe tare da tabbatar da an hukunta masu laifin.

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa, ba za ta bar maganar ba har sai an hukunta waɗanda ke da hannu a kisan gillar.

Bayanai sun nuna cewa an kama mutum 40 da ake zargin su na da hannu kan al’amarin. A ranar Juma’a shafukan sada zumunta musamman a arewacin Najeriya sun cika da fushi da alhini na abin da ya faru a Edo, ɗaya daga cikin jihohin kudancin ƙasar.

Hotunan da aka riƙa yaɗawa sun nuna yadda aka yi wa wasu mutane jina-jina, sannan aka riƙa jefa tayoyin mota a kansu.

Haka nan kuma an ga yadda wasu suke dukan wani mutum da katako a cikin kwalbati, sannan a wani hoton kuma an ga wuta na ci daga can nesa.

Sannan kuma an ga babbar motar kamfanin ɗangote, wadda aka farfasa wa gilashi yayin da wani ɓangare nata ke ci da wuta.

Wani hoton kuma ya nuna bindigogin harba-ka-ruga, irin ta masu farauta ta gargajiya, da kuma adduna.

Bayanai sun nuna cewa mutanen da lamarin ya rutsa da su, waɗanda suka bayyana kansu a matsayin mafarauta, ‘yan sintiri ne suka tare su yayin da suke tafiya a wata babbar mota.

Binciken da ‘yan sintirin suka yi ya sanya aka gano bindigogi a motar, lamarin da ya janyo mutanen gari suka far wa waɗanda ke cikin motar bisa zargin cewa masu garkuwa da mutane ne.

Manhaja ta tattauna da shugaban ‘yan arewa mazauna Edo, Alhaji Badamasi Saleh, wanda ya ce mafarauta 27 ne a cikin motar, inda mutane ne ‘yan arewacin ƙasar waɗanda suka tashi daga garin Fatakwal domin zuwa gida bukukuwan Sallah.

“Lokacin da suka zo garin sai ‘yan bijilante suka tare su, sai suka ce kidinafas ne, suka kama su da duka, suka kashe su, suka ƙona wasu daga daga cikinsu.”

“Mutum 11 suna nan da lafiyarsu amma mutum biyu na jinya a asibiti.”

Yanzu haka dai shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike tare da hukunta waɗanda ke da hannu.

Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo a ranar Litinin ya yi alƙawarin biyan diyya ga iyalan mafarauta 16 da aka kashe.

Ya yi wannan alƙawarin ne a lokacin da ya samu rakiyar takwaransa na jihar Kano, Abba Yusuf, inda ya kai ziyarar jaje ga iyalan mafarautan a Torankawa da ke jihar Kano.

“Muna shirye-shiryen bayar da diyya ga duk waɗanda lamarin ya shafa.

“Ina kuma yaba wa mutanen jihar Kano da ɗaukacin arewa saboda rashin ɗaukar doka a hannunsu da kai harin ramuwar gayya,” inji shi.

Ya yi addu’ar Allah ya jikƙan mafarautan da suka mutu.

Gwamnan Edo ya ƙara, da cewa, tuni aka fara cafke waɗande ake zargi da aikata wannan aika-aika.

“An riga an kama kimanin mutane 14 da ake zargi, za mu ci gaba da bin diddigin lamarin har sai an gurfanar da su a gaban kotu an yi waɗanda aka kashe adalci,” inji Okpebolo.

Shi ma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I Jibrin, a ranar Laraba ya ziyarci ƙaramar Hukumar Bunkure da ke Jihar Kano domin jajenta wa iyalan matafiyan

Sanata Barau ya gana da iyalan mamatan, waɗanda suka fito daga ƙananan hukumomin Bunkure, Kibiya, Rano da Garko, a Masallacin At-Taƙwa da ke Sabon Fegi, Bunkure.

Mai bai wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Isma’il Mudashir, ya bayyana a wata sanarwa cewa Sanata Barau ya tabbatar wa da iyalan mamatan cewa waɗanda suka aikata wannan ta’addanci ba za su tsira ba, domin doka za ta yi aiki a kansu.

Ya ce bayan kama mutum 14 da aka ti da farko, jami’an tsaro sun sake cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan gillan da aka yi wa waɗannan mafarauta.

Sanata Barau ya sanar da bayar da tallafin N1m ga kowanne daga cikin iyalan mamatan 16, wanda jimillar kuɗin ya kai miliyan N16.

Haka kuma, ya bayyana cewa zai gabatar da ƙudiri kan lamarin da zarar Majalisar Dattawa ta dawo zaman ta a ƙarshen wannan wata.

Bayan nuna kaɗuwa da faruwar lamarin, Sanata Barau ya kuma tabbatar wa da iyalai da al’ummar garuruwan cewa za a bi kaɗin haƙƙin ‘yan uwansu da aka kashe tare da yi musu adalci na shari’a.

“Ba za mu ɗauki wannan al’amari da wasa ba. Za mu tabbatar an hukunta waɗanda suka aikata wannan danyen aiki,” inji shi.

A nasa jawabin, Shugaban Limaman yankin, Sheikh Zainul Abidina Auwal, ya gode wa Sanata Barau bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da adalci, tare da bayyana shi a matsayin jagoran da ƙasa ke buƙata domin ci gabanta.

By ukarofi