Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Abin ya soma kamar wasa-wasa, amma yanzu haka dai waɗansu sassan jihohin Kebbi da Sokoto Lakurawa da ‘yan bindiga sun sami gindin zama, inda kuma su ke cin karensu babu babbaka sanadiyyar ko dai da ɗaurin gindin gwamnati ko kuma halin ko oho da ta ke nunawa kan sha’anin tsaro a ƙasar, kamar yadda wasu ke gani.
Jihar Kebbi da ta ke ɗaya daga cikin jihohin da ke sahun gaba a sha’anin tsaro da kuma zaman lafiya yanzu ta shigo cikin jerin jihohin da zaman lafiya da kwanciyar hankali yana neman ya gagara sanadiyyar waɗannan ‘yan bindiga da kuma mayaƙan Lakurawa da ke rajin ɗabbaka shari’ar Musulunci, musamman a waɗansu sassan Jihar Kebbi da suka haɗa da ƙananan hukumomin Arewa da Augie da ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar a Jihar Sokoto.
A baya-bayan nan bayan wani hari da waɗansu mutane ɗauke da miyagun makamai da a ke sa ran Lakurawa ne suka kai a wani shingen binciken jami’an hana fasa-ƙwauri da ke kan garin Bachaka da ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar, inda suka kashe jami’an guda biyu da yaron da ke kama musu aiki, kuma suka ƙona motar ɗaya daga cikin jami’an.
Wakilin Blueprint Manhaja ya kai ziyarar gani da ido kuma ya zanta da waɗansu mutane da ke zaune a wannan yankin.
Wani direba da ke zirga-zirga akan wannan hanyar mai suna Malam Garba ya bayyana wa Blueprint Manhaja cewa, sau da yawa suna ganin ayarin waɗannan mutanen kan babura ɗauke da bindigogi yayin da su ke tafiya, amma dai ba sa tsayar da su kuma ba sa taɓa su kuma suka gan su har suna zuwa cikin kasuwanni suna sayayya ɗauke da bindigoginsu a rataye, sai dai mafi yawanci waɗannan mutanen suna sanye da rawani sun rufe fuskokinsu.
Wani ɗan kasuwa Alhaji Sama’ila Muhammad Ali ya ƙara da cewa, shi sai da yawa su kan sayi kaya a hannunsa kuma ba tare da wata tsangwama ba, sukan sayi kayan masarufi a cikin kasuwa kuma suna biya wani lokacin su kan zo da kuɗin Nijeriya (Naira) ko kuma na Faransa (Saifa) idan suka sayi kaya tun kama daga na abinci har man fetur duk su kan biya.
Wani mutum mazauni ɗaya daga cikin ƙauyukan da ke kusa kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar da bai so a bayyana sunansa ba, saboda dalilan tsaro, ya bayyana cewa, waɗannan Lakurawan sun daɗe suna shigowa ƙauyukansu suna kama dabbobinsu, musamman shanu suna tafiya da su, wani lokacin sukan haɗa da kayan abinci su ɗauka, amma sai dai da wahala su doki mutane ko su yi harbi.
Ya ƙara da cewa, yanzu haka waɗannan mutanen sun kafa sansanoni kusa garuruwansu a saman tsaunuka inda su ke zaune sai dai su kan shigo gari idan suna da buƙatar wani abu su saya su koma.
Sau da yawa idan suka ga mutum yana shan sigari ko sayar da ita sukan ƙwace su karairaya ta su watsar su yi masa wa’azi, wani lokacin ma har suka shiga waɗansu ƙauyuka kamar bayan sallar Isha’i su tara matasan gari suna yi musu wa’azi tare da neman su shigo wannan aikin da su ke yi na jihadi.
Ya bayyana cewa, babban abin da ya ke ɗaga musu hankali shine, yanzu kasuwannin wannan yankin sun soma samun ci baya, saboda fargaba da ‘yan kasuwa ke yi na zuwa wannan yankin duk da ya ke dai ba sa kwace musu kaya kuma ba sa taɓa su.
Wani mazauni ƙauyen Rausa-Kade da ke da ya ce a sakaya sunansa ya ce waɗannan Lakurawan suna da sansani akan wani tsauni da ke kusa da ƙauyen nasu kuma suna ganin su su ma suna ganin su har ma duk suna jin kiran sallar Lakurawan a duk lokacin da suka yi idan ma suna wani nishaɗi suna jin su saboda dutsen yana bayan ƙauyen ne ba nisa.
Wani jami’in hukumar shige da fice da ke aiki a garin Kamba da bai so a bayyana sunansa ba ya shaida wa wakilinmu da cewa, sau da yawa sukan ji harbe-harbe, musamman cikin dare, daga ɓangaren Jamhuriyar Nijar daga inda su ke da shingen binciken da ya ke suna daga ɓangaren Nijeriya ne jefi-jefi, amma dai sukan ɓuya a duk lokacin da suka soma jin irin wannan alamun harbe-harbe saboda tunanin a matsayin su na jami’an tsaro su ke abokan gabarsu.
Yanzu haka bayanai daga waɗannan yankunan musamman daga ƙananan hukumomin Arewa da Augie na nuna cewa, akwai sarakunan da suka kwashe iyalansu inda waɗansu suka yi hijira zuwa Birnin Kebbi ko Argungu suka bar garuruwansu hannun wakilansu da suka haɗa da Ubanƙasar Gumundai da Kangiwa da Lema da Bachaka da Jantullu da sauransu, sai kuma Ubanƙasar Augie da Kwaido daga ƙaramar hukumar mulki ta Augie da ke kan iyakar Jihar Kebbi da Sokoto daga gabas da kuma iyaka da Jamhuriyar Nijar daga yamma.
Wakilin Blueprint Manhaja ya nemi jin ta bakin ko da ɗaya daga cikin sarakunan ne, amma dai hakan ba ta samu ba, saboda a cewarsa daga cikinsu babu wanda ke da hurumin magana da ’yan jarida.
Haka zalika wakilinmu ya nemi jin ta bakin Shugaban ƙaramar Hukumar Mulki ta Arewa, Hon. Sani Aliyu (Kulita), wanda shi ma yana daga cikin shugabannin da suka yi hijira zuwa Birnin Kebbi ta wayar tarho, ya ce, zai kira. Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto bai kira ɗin ba.
Waɗansu bayanai da wakilin Blueprint Manhaja ya tattara suna nuni da cewa, al’ummomin suna kokawa ne jami’an tsaro, saboda a duk lokacin da aka kai hari a wani ƙauye idan an kira jami’an tsaro ba sa zuwa sai bayan sun gama abinda suke yi sun fita da kamar awa uku ko fiye sannan su zo su rinƙa harbin iska, sannan kuma babban abin ban haushi shine, sun fi kowa iya karɓar kuɗi hannun ‘yan kasuwa da direbobi akan hanya.
Hon. Muhammad Hamidu Jarkuka, Kwamishinan Jinƙai da Walwala daga ƙaramar Hukumar Mulki ta Arewa, ya tabbatar da zaman Lakurawan a wannan yankin, inda ya ce, gaskiya ne waɗannan mutanen suna addabar al’ummar wannan yankin, musamman garuruwan da suka haɗa da Jarkuda da Jaja ya ta’allaƙa zuwa ƙasar Kangiwa sune ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar da kuma Sokoto da kuma ƙaramar Hukumar Mulki ta Dandi da kuma Argungu, inda sukan kai farmaki a ƙauyuka daban-daban lokuta daban-daban sai dai ba kasafai sukan buɗe wuta ba sai dai idan sun fuskanci turjiya daga ƙauyawan sukan buɗe wuta suna harbin kan mai uwa da wabi wanda ke sanadiyyar mutuwa ko jikkanta.
Sai dai kwamishinan ya bayyana cewa, bai taɓa samun labarin suna tattara matasan waɗansu ƙauyuka suna jan ra’ayinsu da su shiga wannan ƙungiyar ba, amma dai yana da masaniyar suna cuɗanya da mutanen garuruwan musamman a kasuwanni, inda su ke shiga gari don sayen kayan abinci ko na masarufi.
Ya ƙara da cewa, Gwamnatin Jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Malam Nasir Idris tana iya ƙoƙarin ta wajen ganin an sanar da ingatanccen tsaro saboda a duk lokacin da wani abu ya taso ya kan kira shi kuma ya kan turo jami’an tsaro don su fatattaki maharan.
Haka zalika ya yi kira ga al’umma da su daina jin tsoron hanzarta tseguntawa hukumar da suke kusa da su ba a duk lokacin da suka ga alamun wani tashin hankali ko waɗansu mutane da ba su yarda da su ba, don ɗaukar matakan da ya kamata. Bayan wannan kuma ya kamata a duƙufa wajen karance-karancen Alƙur’ani da roƙon Allah ya yi muna maganin wannan musiba.
Sai dai waɗansu bayanai da wakilinmu ya tattara suna nuni da cewa wannan sace-sacen na dabbobin da ke addabar al’ummar ba Lakurawa kaɗai ke yi ba saboda ana hasashen waɗansu mutane musamman Fulani suna shigar burtu suna kai farmaki ko samame a inda suke shiga gidajen mutane cikin dare suna kama dabbobi suna ajiye su a waɗansu wurare bayan wani lokaci su kai su kasuwanni don sayarwa ko kuma suna yankawa suna kai wa kasuwa ko kuma su kira runzawa (yan fawa) suna sayar musu da nama.
Haka zalika har wa yau dai binciken ya nuna a mafi yawancin garuruwan da ke kan hanya ana ganin wucewar manyan ayari inda ko kwanaki kaɗan kafin sallah an ga wucewar wani babban ayari a garin Argungu a tsakiyar dare da aka ce yawan su zai iya kai su ɗari ko ma fiye akan babura.
Bayan wannan kuma bayanan sun nuna cewa, kullum waɗannan Lakurawan sukan kai hari a ƙauyuka daban-daban a kullum sai dai wanda ya yi muni ko ya yi sanadiyyar harbe-harbe da ya yi muni kaɗai ne ke fitowa fili sanadiyyar tun suna ‘yan kaɗan yanzu sun yi yawan da tarwatsa su zama guda yana da wahalar gaske.
