Tsadar raguna ta sa magidanta watanda

Spread the love

*’Yan kasuwa sun koka da tsadar

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Layya dai wata ibada ce ta yanka dabbobi daga ranar goma ga watan goma sha biyu (Zul-Hajji) zuwa goma sha biyu ga watan da suka haɗa da yanka rago ko tinkiya da raƙumi ko rakuma da  Sa ko saniya da akuya ko bunsuru (ɗan taure) da aka ce ta samo asali ne tun lokacin Annabi Ibrahim Alaikissalam da Allah ya umarce shi da ya yanka ɗan sa Annabi Isma’il Alaihissalam daga baya kuma Allah ya fanshe shi da rago.

Ita dai wannan ibadar sunnah ce mai ƙarfi da aka ɗora kan kowane Musulmi da ke da halin yanka ɗaya daga cikin dabbobin da aka zayyano a sama.

Shekarar bana ta zo da wani yanayi da ba a saba da shi ba musamman na tsadar rayuwa tun kama daga kayan abinci zuwa kayan masarufi na yau da kullum wanda ya sanya yanayin layya ya ɗauki sabon fasali na haɗaka, wanda ake kira watanda, wajen sayen shanu don aiwatar da wannan ibadar ta layya.

Wani magidanci da suka yi irin wannan haɗakar a jihar Kebbi Malam Muhammed Nasir ya bayyanawa wakilinmu da cewa sanadiyyar tsadar raguna ya sanya shi da abokansa suka haɗa naira dubu ɗari-ɗari suka sayi sa na naira dubu ɗari bakwai suka yanka saboda ragon naira dubu ɗari da hamsin bai cika ido ya yi karanta.

Alhaji Hali Bakanike shi ne Sarkin Kara Argungu ya bayyanawa wakilinmu da cewa duk da ya ke dabbobi sun ɗan yi sauƙi amma dai rashin kuɗin ya sanya mutane da yawa haɗaka wajen sayen shanu don aiwatar da wannan ibadar ta layya da ya ke shari’ar musulunci ta yarda haka.

An kawo dabbobi daga wurare daban-daban tun sama da sati biyu babbar kasuwar Argungu ke ci. 

Ana samun raguna tun kama daga naira dubu ɗari da hamsin aƙalla har zuwa ɗari biyar haka-zalika a ɓangaren shanu kuma ana iya samun su daga naira dubu ɗari biyar har zuwa miliyan biyu da ‘yan kai, babban sa da ya fi kowane kuɗi da aka sayar a wannan kasuwar dai ya kai naira milliyan biyu da dubu ɗari biyu.

Wani magidanci ma’aikacin gwamnati Malam Yusuf Sa’idu da bai samu yin layya bana ba ya bayyanawa wakilinmu da cewa gaskiya bana tsadar rayuwa ta hana shi saboda lalurar iyali ta yau da kullum, bayan tsadar rayuwa ga shi kuma albashin da ake bai wa ma’aikata bai taka kara ya karya ba.

Malam Nasiru Abubakar Mera Babban limamin masallacin Sarki Sama’ila Muhammad Mera kuma Mataimakin shugaban majalisar malamai ta ƙaramar hukumar mulki ta Argungu ya bayyana cewa shari’ar musulunci ta yarda da haɗaka wajen layya tun kama daga mutane biyu zuwa bakwai a wajen layya da shanu sai kuma mutane daga biyu zuwa goma a wajen layya da Rakumi muddin ba iyali daya ba ne da ke zaune a ƙarƙashin mutum ɗaya, ma’ana in dai kowa yana cin gashin kan sa ne ya halatta su yi haɗaka wajen layya.

Kafin yanzu malamai sun sha faɗakarwa dangane da halaccin irin wannan layya sai dai saboda mutane suna wadata ba a baiwa wannan fatawar muhimmanci ba sai yanzu da matsin rayuwa ya kai matsi sai aka soma wannan ibadar.

Yanzu idan mutum zai yi layya aƙalla ragon naira dubu ɗari da hamsin zuwa ɗari biyu bai cika ido amma mutane bakwai za su iya haɗa naira dubu ɗari bakwai su sayi sa na naira dubu ɗari bakwai kuma bayan lada za a sami wadataccen nama don iyali.

Ya kuma yi kira ga al’umma musamman wadanda suka yi layya da su yi sadaka da nama ga mabuƙata da mokota da ‘yan uwa kamar yadda Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya ƙwadaitar da al’umma.

Hakazalika masu sayar da raguna a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba sun danganta tsadar ragunan da rashin tsaro da ƙarancin kayan masarufi daga yankin Arewa maso Yamma.

‘Yan kasuwar, a wata hira da aka yi da su yayin wani bincike a kasuwar Abuja, sun ce ƙarancin wadatar su ma ya faru ne saboda rufe iyakokin Nijeriya.

Ahmed Mai-Samari, wani dillalin dabbobi a kasuwar dabbobi ta Dei-Dei, ya shaida wa Manhaja cewa ragunan da ake kai wa manyan biranen sun yi ƙasa da yadda ake tsammani idan aka kwatanta da shekarar 2024, musamman daga ƙasashen makwabta.

“Kun san galibi muna samun waɗannan dabbobi ne daga Nijar da sauran ƙasashen da ke kusa da mu da ke da iyaka da mu a arewa, musamman ma masu matsakaicin girma.

“Yanzu, dole ne mu dogara ga wadatar gida kawai daga manoman dabbobi, wanda ke da iyaka.

“Yan kasuwa da yawa sun bar sana’ar don samun riba mai yawa,” inji shi.

Ya ce farashin raguna ya ninka sau biyu idan aka kwatanta da shekarar 2025, wanda ya danganta hakan ga tsadar sufuri da tsadar rayuwa.

“Ragon da aka sayar da shi kan Naira 200,000 a shekarar 2024 a yanzu ya koma Naira 400,000, masu kuɗi ne kawai ke iya samun sa a yanzu.

“Farashi ya bambanta dangane da girman: ƙananan raguna suna kan Naira 150,000 zuwa Naira 190,000, matsakaita na kan Naira 200,000 zuwa Naira 250,000, yayin da manyan raguna suka kai Naira 350,000 zuwa Naira miliyan daya,” inji shi.

Hakazalika, Mista Sanusi Abdullahi, dan kasuwan dabbobi a gefen titi a Dutse, ya ce farashin raguna ya tashi daga N200,000 zuwa N700,000.

Ya ƙara da cewa samo dabbobin a cikin gida ya kasance mai matukar damuwa da tsada saboda karancin hanyoyin shiga jamhuriyar Nijar, mai yiwuwa sakamakon rikicin siyasa da ake fama da shi.

“Ni da yarana mun yi tafiya daga ƙauye zuwa ƙauye a cikin jihohi daban-daban, mu tattara raguna kuma mu kai su nan. Ba abu mai sauƙi ba,” inji shi.

A kan tallace-tallace, Mista Abdullahi ya bayyana cewa ya sayar da bakwai ne kawai cikin kusan raguna 120 a cikin kwanaki biyu, duk da cewa ya kasance yana da kwarin gwiwar sayar da aƙalla rabin kafin Sallah, ko da ƙarancin riba.

A garin Bwari, wani ɗan kasuwar a gefen titi, Mustapha Aminu, wanda aka fi sani da “Biggie,” shi ma ya koka da yadda ake samun ƙarancin kuɗi, inda ya ɗora alhakin hauhawar farashin kayayyaki da kuma taɓarɓarewar tattalin arziki. 

Ya ce, yayin da da dama cikin Musulmi ke son halartar bikin Sallar Eid el-Kabir, yawancinsu ba za su iya ba.

By ukarofi