Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Ƙungiyar mata a kwalejojin Ilimi (WICE) ta Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya, FCE Gombe, ta gudanar da bikin karramawa ga manyan shugabannin mata da suka taka rawar gani wajen bunƙasa ilimi da ƙarfafa matasa, musamman ‘yan mata.
A wajen bikin, an bai wa Ko’odinetan Shirin AGILE ta Jihar Gombe, Dokta Amina Haruna Abdul, lambar yabo saboda irin gudunmawar da ta bayar wajen inganta ilimi da daidaito tsakanin jinsi.
Dokta Hauwa Haruna ta karɓi kyautar a madadinta.
Shugabar WICE, Hajiya Ramatu Mahdi, ta yaba wa shirin AGILE a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, wanda ta ce ya kawo sauye-sauyen da suka inganta damar ilimin yara mata a Jihar Gombe.
Haka kuma, an karrama Kwamishinar Ilimi ta Jihar Gombe, Farfesa Aishatu Umar Maigari, bisa gudunmawar ta wajen bunƙasa ilimi a jihar.
A jawabinta, Farfesa Maigari ta jinjina wa Gwamna Yahaya kan ƙoƙarinsa na ba wa matasa mata damar cin gajiyar shirin AGILE da sauran tsare-tsaren ilimi.
Sauran waɗanda suka samu lambobin yabo sun haɗa da Dokta Hauwa Yahaya daga hukumar SUBEB da tsofaffin shugabannin WICE.
Bugu da ƙari, an gabatar da tallafin jin ƙai ga tsofaffin mambobin Ƙungiyar a matsayin nuna goyon baya da kulawa.
Taron ya jaddada muhimmancin jagorancin mata wajen tabbatar da cigaba mai ɗorewa a ɓangaren ilimi da al’umma baki ɗaya.
